Daga Rahama Umar Kwaru
Gwamnan jihar kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa zai jagoranci rantsar da sabbin kwamishinoni a ranar litinin 26 ga watan Yuni na shekara ta 2023.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ofishin Sakataren gwamnatin jihar kano Dr. Abdullahi Baffa Bichi a yammacin wannan rana.
Sanarwar tace za’a rantsar da sabbin kwamishinonin ne a dakin taro na Africa House dake gidan gwamnati da misalin karfe 11 na safe.
Wata Kotu a Kano ta hana Abba Gida-gida rushe wasu gine-gine a jihar
Idan za’a iya tunawa a makon da ya gabata ne majalisar dokokin jihar kano ta tantance tare da Amincewa da mutane 17 cikin 19 da gwamnan ya aike mata da sunayen su domin tantancewa.