Wata Kotu a Kano ta hana Abba Gida-gida rushe wasu gine-gine a jihar

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta hana gwamnatin jihar Kano da jami’anta rushe wasu gine-gine da ke kan titin tsohuwar jami’ar Bayero wato BUK Road a kano.

Yadda NAHCON ta Tsara daukar Mahajjatan Nigeria daga Makka zuwa Mina, Arfat da Muzdalifa

Majiyar Kadaura24 Solacebase ta rawaito a ranar Juma’a ne alkalin kotun mai shari’a S. A. Amobeda ya yanke hukunci kan bukatar gaggawar da aka shigar gabansa a madadin Saminu Muhammad, na ya hana gwamnatin Kano rushe kadarorin mai kara wanda ke lamba 41 da 43 Salanta, kan titin BUK, Kano.

Wadanda ake kara sun hada da Babban Lauyan Jihar Kano, Gwamnan Jihar Kano, Gwamnatin Jihar Kano da Ofishin hukumar Kula da Filaye na Jihar Kano.

Sauran sun hada da hukumar kula da tsara birane ta jihar Kano, Babban Sufet ‘Yan Sandan Najeriya, Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, Kwamishinan ‘Yan Sanda, Kwamandan Tsaro da Hukumar Tsaro ta Civil Defence, da Jami’an Tsaro na Civil Defence.

Kotun bayan sauraron bukatar da lauyan mai kara, Farfesa Nasiru Aliyu, SAN ya gabatar, ta bayar da umarnin a gaggauta sauraron karar sannan ta dage karar zuwa ranar 10 ga watan Yuli, 2023.

Tallah

“An ba da wannan umarni na Kotun ne na wucin gadi na hana waɗanda ake ƙara su kansu, da wakilansu, da su guji kutsawa, shiga, mamayewa, ko rushe wuraren da akai kara akan su, wadanda suka hadar da wuri mai lamba 41 da 43 dake Salanta, kan titin BUK, Kano, Wanda takardar shaidar mallaka mai lamba KNMLO8228 da takardar shaidar mallaka mai lamba KNMLO8229 har sai an saurari karar.

 

An dai bada umarnin ne tare da bukatar ma’aikatan kotun da su tabbatar sun sada umarnin kotun ga wadanda ake kara .

Kadaura24 ta ruwaito cewa gwamnan Kano, Abba Yusuf, tun hawansa karagar mulki ya fara rushe wasu gine-gine a jihar wadanda yace an yi zamanin mulki Abdullahi Umar Ganduje ba bisa ƙa’ida ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...