Daga Rukayya Abdullahi Maida
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nigeria NDLEA reshen jihar Neja ta rufe gidan man da ake zargin ana amfani da shi a matsayin wajen boyewa da sayar da tabar wiwi .
Kwamandan hukumar na jihar, Musa Bwalin, ne ya shaidawa manema labarai a Minna cewa an tsare jami’in tsaro da wasu ma’aikatan gidan man domin gudanar da bincike.
Bwalin ya ce sama da shekara guda rundunar ta kama mutane 250 da ake zargi da sayar da miyagun kwayoyi daga cikin 64 da aka samu da laifi.
Wata Kotu a Kano ta hana Abba Gida-gida rushe wasu gine-gine a jihar
Ya kuma bukaci mazauna yankin da su daina kyamar masu shaye-shayen miyagun kwayoyi, maimakon haka jama’a su kusance tare da jan su a jiki ko zasu fahimci matsalolin don gyarawa.

Ya bukaci gwamnan jihar Neja da ya taimaka wa rundunar da motocin aiki domin su samu damar shawo kan matsalar sayar da miyagun kwayoyi a fadin jihar.