Hajjin bana: An Sami masu tabin hankali a Mahajjatan Najeriya, yayin da mutane 6 suka rasu a Saudiyya

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Hukumar kula da aikin hajji ta Nigeria NAHCON tace kimanin Mahajjatan Najeriya guda shida ne suka rasu gabanin fara aikin hajjn bana .

 

Shugaban tawagar likitocin Nigeria a a aikin Hajjn bana Dr. Usman Galadima, ne ya bayyana haka a ranar Asabar a wajen wani taro hukumar ta gudanar a birnin Makkah na kasar Saudiyya.

Yadda NAHCON ta Tsara daukar Mahajjatan Nigeria daga Makka zuwa Mina, Arfat da Muzdalifa

Dr. Galadima ya bayyana cewa, jihohin Osun da Kaduna na aikin Hajjin 2023 kowacce ta rasa mutane bibiyu, yayin da jihar Filato ta rasa mutum daya.

Wata Kotu a Kano ta hana Abba Gida-gida rushe wasu gine-gine a jihar

Ya yi kira ga likitocin da su tabbatar da lafiyar Mahajjatan gabanin fara ibadar don rage yawan mace-macen Mahajjatan, sanann ya kara da cewa ya kamata duk wanda aka ga ba zai iya tafi-tafiyen da za a yi ba to a hana su zuwa .

Tallah

Dr. Galadima ya kuma kara da cewa, tawagar ta kuma gano majinyata 30 da ke fama da tabin hankali, amma a halin yanzu da suna samun kulawar likitoci don ganin sun Sami damar sauke farali a bana .

“Muna ba su kulawar da ta dace, domin a cikin tawagar likitocin mu akwai likitocin kwakwalwa guda hudu. Muna gudanar da aikin da ya dace akan su, kuma muna kyautata zaton zasu yi aikin hajjin bana saboda suna samu lafiya, su kuma dukkansu za su yi aikin hajji saboda suna samun sauƙi ,” in ji Dr. Galadima.

Jami’in ya kuma ce a asibitinsu na alhazan bana, wata mata ta haihu yayin da wasu mata biyu suka yi barna.

Dr. Galadima ya ce hukumar NAHCON ta damu matuka saboda yadda ake cigaba da samun rahoton karaya musamman da Mahajjata masu yawan Shekaru. t

Ya ce tawagar likitocin ta gano mutane takwas da karaya .

A jawabinsa na bude taron, shugaban hukumar Zikrullah Hassan ya ce duk dan Najeriya da yake da ingantaccen bizar aikin hajjin 2023 an dauke shi zuwa kasar Saudiyya ta jirgin sama.

“Mun kawo duk wani dan Najeriya da ke da biza mun kammala kawo su kasa mai tsarki. A wannan garin a yau, muna da ‘yan Najeriya sama da 95,000,” in ji Zikirullah Hassan

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...