Gwamnatin Kano ta magantu kan batun kai Kwankwaso EFCC

Date:

# Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya musanta zargin cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ce ta kai tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ƙarar hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC.

Sanusi Bature ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da gidan rediyon RFI Hausa, inda ya ce gwamnatin Kano ba ta da hannu ko kaɗan a ƙorafin da wasu mutane suka shigar gaban hukumar EFCC kan jagoran tafiyar Kwankwasiyya, wanda kuma ke neman zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar NDC.

IMG 20260704 WA0007
Talla

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ma ta samu labarin shirin EFCC na binciken Kwankwaso ne ta hanyar jita-jitar da ake yaɗawa, yana mai jaddada cewa ba su da alaƙa da wannan batu.

Ya ƙara da cewa gwamnatin Kano tana da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta PCACC, wadda ita ce ke da alhakin gudanar da bincike kan zarge-zargen cin hanci da rashawa a matakin jiha.

Sanusi Bature ya kuma bayyana cewa ba shi ne karo na farko da ake kai ƙarar Kwankwaso gaban EFCC ba, yana mai cewa an sha gayyatar tsohon gwamnan domin amsa tambayoyi kan zarge-zarge daban-daban, tun kafin gwamnatin Abba Yusuf ta hau mulki.

A cewarsa, babu wani tsohon gwamna daga Arewacin Najeriya da ya sha fuskantar gayyata da gurfana a gaban EFCC da ICPC kamar Kwankwaso, saboda haka bai dace a danganta binciken da ake yi masa da gwamnatin Kano mai ci ba.

Ya ce tun daga shekarar 2015 ake kai ƙorafe-ƙorafe kan Kwankwaso, ciki har da batutuwan kuɗaɗen fansho da kuma zargin karɓar kuɗaɗen da suka kai naira miliyan 70 daga ƙananan hukumomi, lokacin da yake fafatawa da Muhammadu Buhari a neman tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa a watan Afrilun 2025, lokacin da yake ƙasar Morocco tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf, Kwankwaso ya kira shi ta waya, inda ya sanar da shi cewa EFCC na shirin gayyatarsa domin amsa tambayoyi.

A cewarsa, bayan wannan kiran ne ya rubuta wata muƙala a jaridu, inda ya nuna damuwarsa kan abin da ya bayyana a matsayin amfani da hukumomin yaƙi da cin hanci wajen matsa wa ‘yan adawa lamba. Ya ce daga bisani ba a sake gayyatar Kwankwaso a wannan karon ba.

Haka kuma, Sanusi Bature ya ce a ƙarshen shekarar da ta gabata EFCC ta sake gayyatar Kwankwaso, inda tsohon gwamnan ya nemi a ba shi damar zuwa ofishin hukumar a ƙarshen mako.

IMG 20260728 WA0005
Talla

Ya bayyana cewa an amince da buƙatarsa, inda ya je ofishin EFCC a ranar Asabar, amma aka tsare shi har ya kwana a can. Sanusi Bature ya ce shi da kansa ya bayar da sunan mutumin da ya je ya tsaya masa wajen karɓar belinsa.

Kwamishinan ya jaddada cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ba ta da hannu a binciken da EFCC ke gudanarwa kan tsohon gwamnan, yana mai cewa hukumar ta sha gayyatar Kwankwaso sama da sau 10 a baya.

LEAVE A REPLY

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Shari’a ta Kano ta sulhunta ƴan siyasar da ke jifan juna da munanan kalamai a

Hukumar Shari'a ta jihar Kano, ta yi zama na...

‎Sanusi Bature Dawakin Tofa: Mutum Mai Manufa, Halaye na Gari da Hidimtawa Al’umma – Falakin Shinkafi

‎Rubutacciyar wasiƙar yabo daga Ambasada Yunusa Yusuf Hamza (Falakin...

‎ ‎Yadda Kwankwaso ya sa na yi rantsuwa da Alqur’ani akan komawa APC – Abba Kabir

‎ ‎Kusan kimanin shekara ɗaya bayan komawarsa jam'iyyar APC mai...

Gwamnan Kano Abba ya yi karin haske kan batun aurensa da yar Kwankwaso

‎A karon farko, gwamnan jihar Kano ya yi ƙarin...