Jam’iyyun adawa za su dakatar da yaƙin neman zaɓe don tattauna yiwuwar haɗe wa a zaɓen 2027

Date:

 

Jam’iyyun siyasa da ke cikin ƙungiyar Coalition for Democracy, ciki har da ADC, NDC da ɓangaren PDP, sun amince za su dakatar da yaƙin neman zaɓensu a faɗin ƙasar ranar 30 ga Nuwamba, 2026.

Jam’iyyun sun ɗauki matakin ne domin halartar taron koli na biyu na ƙungiyar, inda za su rattaba hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa gabanin zaɓen shugaban ƙasa na ranar 16 ga Janairu, 2027.

IMG 20260704 WA0007
Talla

Wata sanarwa da Salihu Moh. Lukman ya sanya wa hannu a madadin jam’iyyun ranar Juma’a ta ce an sauya ranar gudanar da taron daga 23 zuwa 30 ga Nuwamba, bisa buƙatar wasu jam’iyyun saboda yadda ’yan takararsu da kwamitocin yaƙin neman zaɓe suka shiga harkokin kamfen.

Sanarwar ta bayyana cewa dakatar da kamfen na yini guda zai bai wa shugabannin jam’iyyun damar halartar taron baki ɗaya.

Ta ƙara da cewa taron zai mayar da hankali kan kammala yarjejeniyar haɗin gwiwar, tare da tsara matakan da za a ɗauka gabanin zaɓen 2027.

FB IMG

Ƙungiyar Coalition for Democracy dai ta samo asali ne daga taron G100 Opposition Summit da aka gudanar a Abuja ranar 31 ga Agusta, 2026, domin haɗa kan jam’iyyun adawa wajen kare dimokuraɗiyya da tabbatar da gudanar da sahihin zaɓe a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kano Pension App: OGP Ta Kara Tabbata A Kano – Abba Anwar

- Yayin da OGP ke kara karfafa alaka da...

Dokar Yaƙi da Shaye-Shaye: Majalisar Dokokin Kano ta Mayar da Martani ga Muhuyi Magaji

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta mayar da martani ga...

Muhuyi Magaji ya soki majalisar dokokin Kano akan jan ƙafa wajen kafa dokar yaƙi da miyagun kwayoyi

Shugaban kwamitin Kar-ta-kwana kan yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi...

‎ ‎Masana sun ja hankali kan rawar harshen Hausa a fasahar AI da amfanin itatuwa wajen magani

Daga Zulaihat Ahmad Uba ‎ ‎ ‎Masana sun yi kira ga al’ummar...