Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da dakatar da aikin tsaftar muhalli na gobe, Asabar, saboda zaɓen gwaji da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) za ta gudanar.

Read also: A karon farko bayan cire shi daga sakataren gwamnatin Kano Baffa Bichi ya Magantu
Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na Kano, Alhaji Hamza Safiyanu Kachako, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a daren yau.
Read also: Akwai yiwuwar gwamnatin tarayya zata ciyo bashin Naira Tiriliyan 11a shekara ta 2023 – Ministar Kudi
Sanarwar ta ce an ɗauki matakin ne domin ba da damar gudanar da zaɓen gwajin cikin sauƙi, tare da tabbatar da cewa jama’a ba su fuskanci tangarda wajen gudanar da ayyukansu ba.

Gwamnatin ta buƙaci al’umma su lura da sanarwar, tare da ci gaba da kula da tsaftar muhalli a gidajensu da wuraren da suke gudanar da harkokinsu.
Freedom Radio