Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya Koka da yadda ya baiwa jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya kuma suka ci amanarsa.
“Alhamdulillah na gama aiki lafiya, Amma dai Allah ya hada mu da mutane marasa amana, mun ba da gudunmawa daidai gwargwado, Amma an ci amanarmu, Ina baku hakuri ku jira lokaci zai yi da zamu fito da maganganu sala-sala”.
Dr. Baffa Bichi ya bayyana hakan ne lokacin da wasu matasa maza da mata suka taro shi bayan ya dawo daga kasa mai tsarki domin gudanar da ibadar Umara.

Ya ce yanzu ba lokacin magana ba ne, amma idan lokacin yayi matasan za su ji bayanai kala-kala.
” Na gode muku, Ina kuma ba ku hakuri, yanzu ba lokacin magana ba ne, amma muna da maganganu a rubuce muna da su Audio da Bidiyo idan lokacin ya yi za mu fito da su sala-sala”. Inji Baffa Bichi
Dr. Baffa Bichi ya ce zai fito ya fadawa duniya rashin amanar da aka yi masa don gudun kada a kara basu amana, inda ya kira su da masu fadar amana a baki amma kuma ba su da ita a aikace.