2027: An kai wa Ayarin Kwankwaso da Gwarzo Hari a Bichi

Date:

An samu ɓarkewar rikici a ƙaramar hukumar Bichi ta jihar Kano, bayan da wasu gungun mutane ɗauke da makamai suka kai hari kan ayarin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, da ɗan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo.

IMG 20260704 WA0007
Talla

Harin ya faru ne a yayin da tawagar ke ci gaba da rangadin neman goyon bayan al’umma, bayan kammala tarukan gangami a ƙananan hukumomin Tofa, Rimin Gado, Kabo, Gwarzo, Shanono da Bagwai.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun ɗan takarar gwamnan na NDC, Kwamared Ibrahim Garba Shu’aibu, ya bayyana cewa tun kafin tawagar ta isa Bichi, sun fara samun bayanan sirri cewa an tare wasu hanyoyi da nufin hana su gudanar da gangamin siyasa.

A cewarsa, bayan isarsu garin Bichi, sun tarar da alamun tashin hankali da jefe-jefe, inda jim kaɗan bayan sun wuce sakatariyar ƙaramar hukumar ne wasu gungun matasa ɗauke da makamai suka far musu.

FB IMG

Kwamared Shu’aibu ya ƙara da cewa harin ya jikkata wasu daga cikin magoya bayansu tare da lalata motoci, inda ya bayyana cewa ya ga motoci kusan bakwai da aka farfasa a wurin da lamarin ya faru.

LEAVE A REPLY

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

‎Kwamishinan Gidaje na Kano ya tallafa wa mutune 647 a ƙaramar hukumarsa ta Wudil

‎ ‎Kwamishinan Ma’aikatar Gidaje ta Jihar Kano, Arc. Ibrahim Yakubu...

Kotun Daukaka Kara Ta Kammala Shari’ar Rabon Gadon Filayen Baba Nabegu

Hukumar Kamfanin Nabegu Najeriya Limited ta bayyana cewa an...

Da dumi-dumi: Yar Kwankwaso da Gwamna Abba ke Aure ta maka shi a Kotu

Zainab Musa Kwankwaso, mata ta biyu ga Gwamnan Kano,...

An yi wa Tinubu ihun ‘Bama yi’ a Abuja

 Wasu 'yan Najeriya sun yi wa Shugaba Bola Tinubu...