Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya ce ya daina karanta shafukan sada zumunta saboda suna sawa jini na ya hau.
Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da kadaura24 ta gani yayin wani taro.
“ Na dai na karanta kafafen sada zumunta, saboda suna zagi da cin mutunci na, Idan na karanta raina yana baci kuma jini na ya hawa don haka na daina tuba ta. Idan ina son Jin wani abun ya’yana ko ma’aikata na su kan fada min .” Inji Tinubu

Yayin da yake karkare jawabinsa a gangamin yakin neman zabensa da aka gudanar a Jos a ranar Talata, ya sha fama da zamiyar harshe yayin da ya yi kuskuren cewa jam’iyyar PDP a lokacin da ya ke tunanin jam’iyyarsa ta APC.
Hakan dai ya jawo cece-ku-ce a shafukan sada zumunta yayin da masu suka suka yi wa dan takarar jam’iyya mai mulki suka ce bai cancanci zama shugaban kasa ba.
Masu sukar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ta yanar gizo sun ce Tinubu ya kaucewa muhawara domin kada a yi ta tafka magudi