Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci

Date:

Wasu ƙungiyoyi masu goyon bayan jam’iyyar APC a Jihar Kaduna sun yi Allah-wadai da rushe gidan Hon. Mahmoud Sani Sha’aban Dan Buram Zazzau, tsohon ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar mazaɓar Sabon Gari, Zariya, daga shekarar 2003 zuwa 2007.

Gidan, wanda ke lamba 3, Titin Churchill, GRA, Zariya, an rushe shi ne a lokacin da ake ci gaba da shari’a kan wata takaddamar bashi tsakanin tsohon ɗan majalisar da Alhaji Abubakar, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce da kiraye-kirayen neman adalci.

FB IMG

Rahotanni sun nuna cewa rushe gidan ya faru ne duk da cewa ana zargin akwai umarnin kotu kan lamarin, wanda ya sa magoya bayan tsohon ɗan majalisar da mazauna yankin nuna damuwarsu.

Bayan faruwar lamarin, wasu mazauna yankin da magoya bayan Sha’aban sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna rashin jin daɗinsu, tare da kira ga hukumomin da abin ya shafa da su shiga tsakani domin tabbatar da bin doka.

Da yake bayyana matsayinsa kan lamarin, Hon. Ahmad Dan Premier, kodinetan ƙungiyar Bola Ahmed Tinubu for President Ambassadors a Jihar Kaduna, ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da shugabannin APC da sauran masu ruwa da tsaki da su gaggauta shiga tsakani.

Ahmad Dan Premier ya yi wannan kiran ne yayin da ya jagoranci mambobin ƙungiyarsa zuwa gidan Hon. Sha’aban da ke GRA, Zariya, domin jajanta masa da nuna goyon baya.

Ya bayyana cewa, idan aka yi la’akari da gudummawar da Sha’aban ya bayar wajen bunƙasa APC a Jihar Kaduna, ya kamata shugabannin jam’iyyar da mambobinta a faɗin ƙasar nan su nuna damuwa kan lamarin.

“Idan aka yi la’akari da gudummawar da Sani Sha’aban ya bayar wajen ci gaban jam’iyyarmu ta APC a Jihar Kaduna, muna ganin ya dace mambobin APC, ba kawai a Jihar Kaduna ba, har ma a faɗin Najeriya, su nuna tausayi bisa wannan mummunan lamari.

“Wannan na ɗaya daga cikin manyan abubuwa masu tayar da hankali da kuma ban tausayi da na taɓa gani a rayuwata,” in ji shi.

Haka kuma, wakilan ƙungiyoyi daban-daban, ciki har da ƙungiyoyin fararen hula, mafarauta, makanikai, ’yan kasuwa da ƙungiyoyin Kiristoci da Musulmi, sun bayyana alhininsu kan rushe gidan.

Sun kuma yi kira da a tabbatar da adalci tare da bin matakan doka wajen warware takaddamar da ta haddasa lamarin.

Da yake mayar da martani, Hon. Mahmoud Sani Sha’aban ya gode wa waɗanda suka ziyarce shi tare da nuna damuwa da tausayawa kan abin da ya faru.

Ya ce batun yana gaban kotu, yana mai nuna rashin jin daɗinsa kan yadda aka rushe gidan a lokacin da ake ci gaba da shari’a.

“Wannan lamari yana gaban kotu, amma duk da haka sai suka ɗauki doka a hannunsu. A yanzu babu abin da zan ce face ci gaba da addu’a ga Allah Maɗaukakin Sarki domin Ya kawo ɗaukinsa,” in ji Sha’aban.

Ya ƙara da cewa, a matsayinsu na ’yan Adam kuma Musulmai, ya kamata su kasance masu haƙuri da yarda da ƙaddarar Allah, yayin da suke jiran sakamakon shari’ar.

Sha’aban ya bayyana cewa a halin yanzu yana jiran hukuncin kotu kan takaddamar, yana mai cewa ba shi da wani ƙarin bayani da zai yi kan lamarin a wannan mataki.

IMG 20260704 WA0007
Talla

← Back

Thank you for your response. ✨

Idan za a tuna, rushe gidan ya faru ne a lokacin da ake ci gaba da shari’a kan takaddamar bashi tsakanin Alhaji Abubakar da Hon. Mahmoud Sani Sha’aban.

Sai dai ana sa ran hukumomin da abin ya shafa za su gudanar da bincike tare da tabbatar da cewa an bi doka wajen warware takaddamar.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

‎Kwankwasiyya ta zargi wata ma’aikaciyar INEC a Kano da canja sunayen ƴan takarar NDC

‎ ‎Ƙungiyar siyasa ta Kwankwasiyya ta zargi wata ma'aikaciyar INEC...

‎Jerin Jihohi 20 da Tinubu ba zai samu damar zuwa kamfen ba

‎ ‎Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai halarci gangamin yaƙin...

‎Kungiyar tsofaffin kantomomi t shekarar 2024 ta gudanar da saukar Alqur’ani da addu’o’i domin neman nasarar gwamna Abba

‎Babbar kungiyar tsofaffin Kantomomin riƙon ta shekarar 2024 ta...

Ba zan iya zuwa yaƙin neman zaɓe a kowace jiha ba – Tinubu

‎Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ba zai...