Daga Hafsat Lawan Sheka
Ayarin wasu lauyoyi har sama da 200 daga jihohin arewacin Nigeria 19, sun gargadi Shugaban kasa Bola Tinubu da kotun ƙolin Nigeria game da Shari’ar gwamnan jihar kano dake gaban kotun ƙoli a halin yanzu.
“Mun damu kawai da gaske dangane da abin da ya faru a Kotun daukaka kara na hukuncin da ta yanke na zaben gwamnan jihar Kano a 2023, inda suka dage cewa dole ne a bi doka don tabbatar da kuri’un kowane dan Najeriya a lokacin zabe”.

Da yake magana a madadin lauyoyin da ke karkashin tutar Abba Kabir Yusuf Volunteer Lawyers Forum For The 19 – Northern Jihohin da kuma Abuja a wani taron manema labarai da suka gudanar a Arewa House Kaduna ranar Lahadi, Barista Yusuf Ado Ibrahim ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kotun koli bai kamata a bar Najeriya ta zama kasar jam’iyya daya ba domin hakan ya sabawa ka’idojin dimokuradiyya .
“A tarihi, idan aka yi la’akari da tsohuwar Nijeriya, shugabanninmu na baya irin su Sir Ahmadu Bello masu albarka da sauran su a kodayaushe suna mutunta doka da tsarin dimokuradiyya, a don hakaka ne muke kira ga shugaban mu, Bola Ahmed Tinubu da bangaren shari’a su mutunta doka kuma su bijirewa yunkurin gudanar da tsarin jam’iyya daya a Nijeriya, tare da ba da tabbacin kuri’un duk wani mai zabe a Nigeria sun yi amfani a lokaci zabe kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 ya tanada.
Zargin Almundahana: Yan sanda sun kama wani hadimin gwamnan Kano
Wannan ba ya rasa nasaba da yadda mutanen Kano nsuka kada kuri’ar goyon bayan gwamna Abba Kabir Yusuf domin ba shi damar ci gaba da ayyukan alherin da zasu kara inganta rayuwar al’ummar jihar Kano,” inji kungiyar.
Kungiyar a wajen taron, ta kuma bukaci a sake fasalin dokar zabe.
“Yana da kyau a bayyana a nan cewa dokar zabe na bukatar sake yi mata gyare-gyare domin magance wadannan matsalolin da suka shafi tsarin shari’a da dimokuradiyya, ya kamata a ce ana gama duk harkokin Shari’ar Zaɓe kafin rantsar da wadanda suka lashe zaben don gudun sake faruwar irin Wadannan abubuwan.

“Batutuwan sun yi yawa da ba za a iya ambata ba. Amma dukkanmu muna zaune a nan mun yi imani da karfi na tsarin shari’a mai ‘yanci. Mun yarda da gazawar alkalan mu a matsayinmu na mutane, muna fatan kotun koli za ta yi abin da ya dace wajen yanke hukunci ba tare da kokarin dadadawa wani ko wasu ba”.
“Muna fatan cewa za a kare martabar talakawan jihar Kano tare da mutunta zabinsu, muna kuma da yakinin cewa Kotun Koli za ta yi adalci ta hanyar tabbatar da bayyana cewa zababben Gwamnan Jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, wanda jama’ar jihar Kano shi ne yayi nasara .