Ba zan iya zuwa yaƙin neman zaɓe a kowace jiha ba – Tinubu

Date:

‎Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ba zai iya raka mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC zuwa dukkan wuraren da za su gudanar da kamfen gabanin zaɓen 2027 ba.
‎
‎Tinubu ya ce akwai abubuwan da suke buƙatar ya mayar da hankali kan gudanar da su a lokacin da ake yawon kamfe din.

IMG 20260704 WA0007
Talla

‎
‎Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Abuja, yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, inda ya buƙaci mambobinsa su kai saƙon jam’iyyar ga ƴan Najeriya a faɗin jihohi da ƙananan hukumomi.
‎
‎Shugaban ya ce ya amince da shawarar cewa bai kamata yaƙin neman zaɓe su ɗauke masa hankali daga gudanar da mulki ba, yana mai cewa Najeriya na buƙatar kulawarsa a halin yanzu.
‎
‎“Kun gargaɗe ni da kada wahalhalun yaƙin neman zaɓe su ɗauke min hankali daga gudanar da mulki, kuma na amince da wannan shawara. Najeriya na buƙatar kulawa sosai a yanzu,” in ji shi.
‎
‎Tinubu ya buƙaci mambobin kwamitin su fahimci cewa ba zai iya kasancewa tare da su a dukkan wuraren da za su gudanar da kamfen ba, saboda gwamnati na da wasu kuɗaɗen da za ta biya da kuma wajibai na kuɗi ga ƙasashen waje.
‎
‎Ya ce: “Don haka, ku yi haƙuri idan ba zan iya zuwa ko’ina tare da ku ba. Muna da kuɗaɗen da za mu biya, kuma masu bin mu bashi daga Amurka ba za su jira ba.”

FB IMG
‎
‎Shugaban ya kuma ce gwamnatinsa na buƙatar jawo hankalin masu zuba jari da za su zuba kuɗaɗensu a Najeriya na dogon lokaci domin samar da kyakkyawar makoma ga ’ya’yan ƙasar.
‎
‎Ya ce yana son masu zuba jarin su zo Najeriya su zauna, su kuma zuba jari domin amfanin al’umma da kuma makomar yara.
‎

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-Yanzu: : INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

‎ ‎Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta...

NDLEA Ta Kama Mutane 1,860, Ta Kwace Ton 5.4 na Miyagun Ƙwayoyi a Kano.

‎ ‎Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta...

‎Karin kudin haya: Magidanta dake haya sun nemi a gajin gwamnatin Kano

‎ ‎ ‎ Magidanta dake zaune a gidajen haya a Kano...

TikTok ya magantu kan takaita amfani da shafin a Arewacin Nigeria

 Kamfanin TikTok ya musanta cewa shi ne ya takaita...