‎Kungiyar tsofaffin kantomomi t shekarar 2024 ta gudanar da saukar Alqur’ani da addu’o’i domin neman nasarar gwamna Abba

Date:

‎Babbar kungiyar tsofaffin Kantomomin riƙon ta shekarar 2024 ta gudanar da taron addu’o’i na musamman domin neman zaman lafiya mai ɗorewa da neman Allah ya baiwa gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf nasara a zaben 2027.
‎
‎An gudanar da taron addu’ar ne a ranar Alhamis, 15 ga Oktoba, 2026, a zauren Coronation Hall da ke gidan gwamnatin Kano.

IMG 20260704 WA0007
Talla

‎
‎Taron ya samu halartar mambobin ƙungiyar, ciki har da tsoffin kansiloli, sakatarorin ƙananan hukumomi da shugabanninsu daga dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar.
‎
‎A yayin taron, mahalarta sun sauke Alƙur’ani mai girma da kuma gudanar da addu’o’i na musamman, inda suka roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da ya kawo zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankali a Jihar Kano da Najeriya baki ɗaya, musamman yayin da ƙasar ke shirin tunkarar babban zaɓe mai zuwa.
‎
‎Da take jawabi a wajen taron, Hajiya Balkisu Yakubu Indabo ta yi kira ga al’umma da ’yan siyasa da su rungumi zaman lafiya, haƙuri da haɗin kai, domin ganin jam’iyyar APC ta samu nasara a zaɓukan da ke tafe.
‎
‎Ta jaddada cewa samar da yanayin zaman lafiya ne kaɗai zai ba da damar cimma kyakkyawan sakamako a harkokin siyasa da zaɓe.
‎
‎ta ce sun shirya taron ne don rokon Allah ya baiwa gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da dukkanin yan jam’iyyar APC Nasara a zaben 2027 dake tafe.
‎
‎” Mun shirya tsaf domin ganin mun fito da magoya bayanmu domin zabar dukkanin yan takarar jam’iyyar APC daga sama har kasa , daga kasa har sama”. Inji Bilkisu Indabo

FB IMG
‎
‎Bilkisu Indabo wacce take tsohuwar kantoma ce ta karamar hukumar Wudil, ta ce Kantomini guda 31 ne suka biyo gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf cikin jam’iyyar APC.
‎

Bayan kammala saukar da addu’o’ an yanka sa Wanda za a yi Sadaka da shi, domin Allah ya amsa rokon da aka yi.
‎

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ba zan iya zuwa yaƙin neman zaɓe a kowace jiha ba – Tinubu

‎Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ba zai...

Yanzu-Yanzu: : INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

‎ ‎Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta...

NDLEA Ta Kama Mutane 1,860, Ta Kwace Ton 5.4 na Miyagun Ƙwayoyi a Kano.

‎ ‎Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta...

‎Karin kudin haya: Magidanta dake haya sun nemi a gajin gwamnatin Kano

‎ ‎ ‎ Magidanta dake zaune a gidajen haya a Kano...