Farfesa Isa Ali Pantami ya bai wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) wa’adin kwana biyu ta wallafa sunansa a matsayin ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyar PDP a zaɓen 2027.
Read also: DA DUMI-DUMI: Kwamishinan Sufuri na Kano ya yi murabus saboda takaddamar belin dilan kwaya
Lauyoyinsa ƙarƙashin jagorancin Ahmed Raji, SAN, sun aika wa hukumar takardar ƙorafi ranar Litinin, 12 ga Oktoba, 2026, bayan cire sunan Pantami daga jerin sunayen ’yan takarar da INEC ta wallafa ranar 10 ga Oktoba.

Lauyoyin sun ce Pantami ya lashe zaɓen fitar da gwani na PDP da aka sake gudanarwa ranar 29 ga Satumba, bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta soke zaɓen farko tare da umartar jam’iyyar ta sake gudanar da shi cikin kwanaki 30.
Read also: Kwankwaso ya yi zazzafan martani ga rundunar yansada kan Maulidin Inyass na Kano
Sun ƙara da cewa jami’an INEC sun halarci sabon zaɓen domin sa ido, kuma an miƙa sunan Pantami ga hukumar a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.
A cewar lauyoyin, cire sunansa ba tare da bayyana dalili ba ya saɓa wa tsarin doka, inda suka buƙaci INEC ta gyara lamarin tare da sanar da su a rubuce kan matakin da ta ɗauka.

Read also: Zabin Musulmi da Kirista a baya bai amfanawa Yan Nigeria komai ba – Oshomole
Sai dai, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, INEC ba ta mayar da martani kan ƙorafin ba.
Pantami, tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani na Nijeriya, na neman tikitin PDP domin takarar gwamnan Gombe a zaɓen 2027.