Kwankwaso ya yi zazzafan martani ga rundunar yansada kan Maulidin Inyass na Kano

Date:

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga rundunar ƴansandan Najeriya su dinga amfani da ƙwarewa, da kaucewa bayanan da ka iya tada hankali yayin gudanar da ayyukansu, musamman a jihar.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, hakan na zuwa ne bayan damuwar da aka nuna kan sanarwar ‘yan sandan jihar Kano na yiwuwar za a kai harin ta’addanci a jajibaren bikin Mauludin da mabiya ɗarikar Tijjaniyya suke gudanarwa a duk shekara, da aka shirya yi a filin wasa na Sani Abacha da ke jihar.

InShot 20250115 195118875
Talla

 

Kwankwaso ya bayyana hakan a shafinsa na X, inda ya ƙara da taya mabiya ɗarikar Tijjaniyya da gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da Sarki Sanusi Lamido Sanusi II, kan nasarar yin taron Maulidin lami lafiya.

Jaafar Jaafar ya fallasa sunan mai kitsawa gwamnatin Kano makarkashiya a Abuja

A makon da ya wuce ne dai, rundunar ‘yansandan jihar Kano ta fitar da sanarwar gargaɗi kan barazanar kai harin ta’addanci a jihar, da buƙatar a dakatar da bikin Maulidin da yake tara ɗaruruwan mutane daga sassan jihar da jihohi makofta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...