Ma’aikatan Gidan Rediyon Najeriya (FRCN) guda biyu sun samu gurbin shiga shirin horaswa na shekarar 2026 mai suna UK Media Excellence for Emerging Technology (UK-MEET) Fellowship, wanda aka tsara domin ƙarfafa ƙwarewar ’yan jarida wajen bayar da rahotanni kan sabbin fasahohin zamani.
’Yan jaridar su ne Chinasa Ossai, editan labaran intanet a hedikwatar FRCN da ke Abuja, da Khadijah Aliyu, ’yar jarida a gidan rediyon Radio Nigeria da ke Kano.

An zaɓe su ne bayan tantance masu neman shiga shirin, inda aka samu sama da mutane 500 daga cikin ’yan jarida da masu ƙirƙirar abubuwan yaɗa labarai a Najeriya da Ghana.
Kwalejin Imperial da ke Landan ce za ta gudanar da shirin ta hannun Imperial Global Ghana, tare da tallafin Babban Ofishin Diflomasiyyar Birtaniya a Ghana.
A cewar masu shirya shirin, kashi 13 cikin ɗari ne kawai na waɗanda suka nemi gurbin suka samu nasarar shiga, inda aka bai wa ƙwararru biyu damar tantance kowace takardar neman shiga da ta cika ƙa’idojin shirin.
Shirin na da manufar ƙarfafa ƙwarewar ’yan jarida wajen bayar da rahotanni kan sabbin fasahohin zamani, ciki har da sabuwar Fasahar (AI), fasahohin da suka shafi sauyin yanayi da kuma sabbin hanyoyin inganta kiwon lafiya.
Za a gudanar da shirin na musamman a Abuja, inda waɗanda aka zaɓa za su gana da masu bincike, gudanar da masu aikin jarida da kuma samar da sabbin dabarun labaran da za su rubuta.
A yayin horaswar, mahalarta za su koyi hanyoyin tantance sahihancin ikirari kan sabbin fasahohi, gano bayanan da ke ƙarfafa sakamakon binciken kimiyya, da kuma bayyana bayanai masu sarkakiya cikin sauƙin da jama’a za su fahimta.
Za a kuma yi la’akari da ’yan jaridan da suka nuna ƙwarewa wajen amfani da abubuwan da suka koya tare da samar da ingantattun shawarwarin labarai, domin ba su damar shiga wani shirin musayar ilimi a Landan, Birtaniya, a ƙarshen watan Nuwamba.
Ana sa ran shirin zai ba waɗanda aka zaɓa damar tattaunawa da masu bincike a Kwalejin Imperial da kuma samun fahimtar kai tsaye game da kimiyyar da ke bayan labaran da suke son gudanarwa.
Chinasa Ossai na bayar da rahotanni kan kimiyya, kirkire-kirkire da fasahohi a aikinta a FRCN, inda take taimakawa wajen fahimtar da jama’a sabbin abubuwan da ke faruwa a waɗannan fannoni da kuma muhimmancinsu ga ci gaban ƙasa.
Ita kuwa Khadijah Aliyu, wadda ke aikinta a Kano, tana da sha’awar bayar da rahotanni kan ci gaban kimiyya, fasahohin zamani da kirkire-kirkiren da ke taimakawa wajen magance matsalolin al’umma da inganta rayuwar jama’a.
Read also: Jerin Sunayen Yan Majalisun Kano da suka bi sahun gwamna Abba
Read also: Matsalar tsaro, tasa Gwamnatin Jihar Zamfara ta dakatar da taron kungiyar yan Jaridu NUJ a Jihar

Zaɓen ’yan jaridar biyu ya nuna muhimmancin aikin jarida na musamman wajen isar da ilimin kimiyya ga jama’a cikin sauƙi, bincikar sahihancin ikirari kan sabbin fasahohi da kuma nazarin yadda kirkire-kirkire ke shafar rayuwar al’umma.
Shirin zai kuma ba su damar ƙara ƙwarewa a aikin jarida, tattaunawa da masana bincike da kuma gano sabbin hanyoyin bayar da rahotanni kan fasahohin zamani da tasirinsu ga ci gaban Najeriya.