Gina Jami’oi masu Zaman kansu zaisa dalibai samun guraben Karatu – Sarkin Kano Bayero

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, CNOL, yayi kira ga mawadata da su tallafawa kokarin gina Jami’oi masu zaman kansu da wasu mawadata keyi a jihar Kano.

 

Alhaji Aminu Ado Bayero yayi wannan kiran ne a wajan taron kaddamar da littafin tarihin rayuwar Suhugaban rukunin kamfanonin AZMAN Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina wanda aka yiwa lakabi da (RESILIENCE) aka kuma gudanar da taron a dakin taro na Jami’ar Bayero dake Kano.

 

A Cikin sanarwar da sakataren yada labaran Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24, yace martaba Sarkin yace gina irin wadannan jami’oi a masu Zaman kansu a jihar Kano zai taimakawa dalibai su samu guraben karatu bayan kammala makarantun sakandire

.

A don hakane ma ya yabawa Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina bisa samar da wannan jami’a, yana mai cewa hakan zai cigaba da habaka ilimi a jihar Kano, tareda godewa wadanda suke akan gaba wajan gina irin wadannan jami’oi masu Zaman kansu.

 

Talla

Alhaji Aminu Ado Bayero yace a shekaruna baya an samar da kamfanonin jiragen Sama wadanda suka hadar Kabo da Freedom da IRS air, inda yace yanzu kuma akwai Azman da Rano air, kuma dukkaninsu kamfanonin jirage ne na “yan asalin jihar Kano.

 

Yayi bayanin cewa suna bayar da gudummawa kwarai da gaske, amma yaja hankalin kamfanonin jiragen da suka rage suyi duba na tsanaki domin dubawa da gyara irin kura kuran da aka samu a baya domin samun nasara.

 

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero daga bisani yayi Kira ga al’uma su cigaba da jajircewa wajan yiwa Nageria addu’oin samun Zaman lafiya da hadin kan al’umar wannan kasa, ya kuma yi addu’ar zabuka masu zuwa Allah yasa ayisu lafiya a gama lafiya tareda zaba mana shugabanni nagari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...