Zargin badakala: Ka fito ka fasa kwan, in ka ki mu fasa maka mugunya- Waiya ga Baffa Bichi

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Gwamnatin Jihar Kano ta kalubalanci tsohon sakataren gwamnatin jiha Dr. Baffa Bichi da ya fito ya bayanan abinda yake da shi wanda aka aikata cin hanci da rashawa ko aikata ba dai-dai ba, tana mai cewa matukar ya gaza fito da hujjoji to ita za ta fito da ta shi badakalar.

“Badakala ce ta sa aka Kore shi daga sakataren gwamnatin jihar Kano, amma saboda kara irin ta mai girma gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce a fadawa duniya saboda rashin lafiya aka sallame shi”.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Kwamishinan ƴan labarai da harkokin cikin gida na Jihar Kano kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya yi kalubalen a taron manema labarai a nan Kano ranar Juma’a da yamma.

Gwamnatin ta ce tana da bayanai na badakalar kudi da yayi a ayyukan sa a gwamnatin jihar Kano da hukumar Bada tallafin karatu ta gwamnatin tarayya TETFUD wacce hakan ta sa aka kore shi daga aiki.

Rikicin Masarautar kano: Yansanda sun garkame gidan Galadiman Kano

“Kada tsohon sakataren gwamnatin ya manta cewa ba rashin lafiyar sa ne kawai yasa aka kore shi daga sakataren gwamnati ba, harma da badakalar karkatar da Shinkafa da makusantansa su ka yi wanda ana zargin ya na da hannu a ciki,” inji Waiya.

Kwamishinan ya ce matukar Dr. Baffa Bichi da sauran yan jam’iyyar APC na jihar Kano ba su saisaita kalamansa ba, to gwamnatin za ta bankado wasu badakaloli da aka tafka a zamanin mulkin Ganduje.

InShot 20250309 102403344

” A gwamnatin Abba Kabir Yusuf ba bu wasu shafaffu da mai, sabanin gwamnatin Ganduje da shi da mai daukinsa da wasu mutane biyu ne kadai suke iya yanke me za a yi a gwamnatin, sabanin yanzu da ake komai bisa chanchanta”. A cewar Waiya

“Tun da aka kirkiri jihar Kano ba’a taba yin gwamnatin jiha a Kano da ta yi Al’mundahana da wawure dukiyar al’umma kamar gwamnatin APC ta shekaru 8 a jihar Kano ba, Amma wai Baffa Bichi da ya saka yaransa suka wawure dukiyar al’umma shi ne zai ce yana da bayanan da wasu suka aikata ba dai-dai ba,” inji Waiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...