Kadan ya rage da na nada Aminu Ado a matsayin Sarkin Kano – Kwankwaso

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso kuma Jagoran tafiyar Kwankwasiyya na kasa ya bayyana Sarkin Kano Aminu Ado Bayero a matsayin mutum mai karamci da ya kusa nada shi Sarkin Kano a shekarar 2014.

 

Kwankwaso ya bayyana hakan ne ga wani makusancinsa da ya nemi jaridar Nigeriantraker ta sakaye sunansa a yayin wani taro da aka yi jim kadan bayan rantsar da Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan Kano.

 

Kwankwaso, tsohon Sanatan Kano ta tsakiya ya kara da cewa a duk lokacin da ya hadu da Sarkin Kano ko a wani taro ko ba a wajen taro ba, Sarkin ya kan gaishe shi da girmamawa.

Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya yi sabbin nade-naden mukamai

“Ba ni da wata matsala da shi, na kusa nada shi Sarkin Kano amma Allah bai so a wancan lokacin .

Wata haduwa da Kwankwaso sukai da Sarkin Kano Aminu Ado Bayero a filin jirgin sama

Gwamnatin tarayya ta wancan lokacin ce ta bani haushi shi yasa na nada Sanusi ba don ya kwanta min ba, sai don in cusawa su Jonathan da mutanensa bakin cikin saboda ba ma jituwa da su.

Gwamnatin Kano za ta rushe Masarautun Gaya, Rano, Bichi da Karaye da Kuma dawo da Sarki Sunusi

Gaggawa da waccan gwamnatin ta yi na taya Lamido Sanusi Ado Bayero a matsayin Sarki ya sa ni baci rai, hakan ta sa na yanke shawarar nada Sanusi Lamido a matsayin Sarkin Kano.

Majiyar da ta nemi a sakaya sunanta ya ce ba ya tantama kan sahihancin wanann labari da suka tattaunawa a tsakaninsu da Kwankwaso .

Kafin in bar gwamnati sai da na tura masa wasu jami’an gwamnati a kan abun da yake rabawa bayan ya tara su a fadarsa duk kuwa da yasa mun hana bara a wancan lokacin a jihar kano.”

Mun jawo hankalinsa ya daina ba su kudi, saboda hakan kamar yana baiwa mabaratan goyon baya ne, amma ya yi kunnen uwar shegu”. Majiyar ta ce

Tsohon gwamnan ya shaida wa majiyar Nigeriantraker cewa, tsohon Sarkin Kano na 14 ya samu matsala da Kwankwaso a Zangon mulkin Kwankwaso na farko matsayin gwamnan Kano har ta kai ga tsohon gwamnan ya rufe asusun gwamnatin jihar Kano a bankin United Bank for Africa.

Sanusi a lokuta daban-daban ya ƙalubalanci Kwankwaso ta fannoni daban-daban har ma da tsarin sa na tafiyar da tattalin arzikin jihar kano a wancan lokacin.

Idan dai za a iya tunawa an nada Sarkin Kano Muhammad Sunusi na biyu a ranar 8 ga watan Yuni bayan rasuwar Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero.

Daga nan sai Gwamna Kwankwaso ya kaucewa matsin lambar da aka yi masa na nada dan Alhaji Ado Bayero Alhaji Sunusi Ado Bayero a kan karagar mulkin Kano, amma ya baiwa tsohon Gwamnan CBN Sunusi Lamido Sunusi da aka dakatar.

Tun bayan rantsar da Abba Kabir Yusuf ake ta cece-ku-ce a fadin Kano kan yiwuwar sake dawo Sarki Muhammad Sunusi na biyu a matsayin Sarkin Kano, amma gwamnati da majalisar dokokin jihar sun musanta labarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...

Na riga Kwankwaso shiga harkokin Siyasa – Sanata Barau Jibrin

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jaridun Amurka sun bankado Tsare-tsare uku da sojojin Amurka ke yi don tunkarar Najeriya

Rahotanni daga wasu jaridun Amurka na bayyana cewa rundunar...

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...