Kwankwasiyya ta kai ƙorafi kan zargin amfani da kotuna wajen muzgunawa yayanta a Kano

Date:

Ƙungiyar Kwankwasiyya ta shigar da ƙorafe-ƙorafe ga Babban Alkalin Jihar Kano da Hukumar Kula da Ayyukan Shari’a ta jihar kan zargin nuna bambanci da siyasantar da wasu matakan shari’a.

A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ranar Litinin, 28 ga Satumba, 2026, ta ce ta damu da abin da ta bayyana a matsayin zargin amfani da hanyoyin shari’a wajen takura wa wasu da ke da alaƙa da Kwankwasiyya, NDC da sauran masu ra’ayin adawa a jihar.

IMG 20260704 WA0007
Talla

Ƙungiyar ta ce ƙorafe-ƙorafen ba na neman tsoma baki cikin ’yancin kotuna ko yanke hukunci kan shari’o’in da ke gabansu ba, sai dai tana neman a gudanar da bincike kan yadda ake gudanar da wasu shari’o’i a Kotunan Majistare da na Shari’a.

“Ƙara ce mu ka kawo ta Alkali Muhammad Sharama na kotun Shari’a ta Ungoggo saboda ya daure mana mutane biyu, Abba Usama Ibrahim, AIHA da kuma Alhaji Murtala Dawanau, wanda wannan abu da ya yi zalunci ne”.

Kwankwasiyya ta kuma gabatar da wani zargi da ta danganta ga Babban Lauyan Jihar Kano, inda ake zargin an yi magana kan yiwuwar amfani ko tasiri kan wasu jami’an shari’a wajen hukunta mutanen da ake ganin suna goyon bayan Kwankwasiyya da sauran ’yan adawa.

Ƙungiyar ta ce ta kuma nemi a binciki zargin cewa wasu magoya bayan Kwankwasiyya da aka kama aka gurfanar za a hana su beli har zuwa bayan babban zaɓe mai zuwa.

Sai dai ƙungiyar ta jaddada cewa ba ta gabatar da waɗannan zarge-zargen a matsayin tabbatattun hujjoji ba, tana mai neman a gudanar da bincike mai zaman kansa da adalci domin tabbatar da gaskiyarsu.

Ta ce babban abin da take nema shi ne daidaito a gaban doka da kuma rashin son kai a harkokin shari’a, tare da kira ga bangaren shari’a da ya kasance ba ya karkashin matsin lambar siyasa.

Ƙungiyar ta ce duk wani lamari da ya wuce ikon bangaren shari’a ya kamata a mika shi ga hukumomin da abin ya shafa.

FB IMG

Sanarwar ta ƙare da cewa matakin da ta ɗauka kira ne ga sa ido, gaskiya, rikon amana da kuma tabbatar da daidaitaccen amfani da doka, tana mai cewa bai kamata siyasa ta zama dalilin kamawa, gurfanarwa, tsoratarwa ko nuna bambanci a harkokin shari’a ba.

Sanarwar da ƙungiyar ta fitar tana ɗauke ne da sa hannun Yusuf Ibrahim Kofarmata a madadin ƙungiyar Kwankwasiyya.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Fadar shugaban kasa ta bayyana ainahin halin da Tinubu ya ke ciki

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu...

Shin da gaske ne Sarki Sanusi ya ci amanar tsohon Gwamnan Kaduna? -Matar El-Rufai ta yi bayani

‎Matar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, Asia Mohammad...

‎Majalisar Zartarwar Kano Ta Amince Da Kashe Naira Biliyan 144 Kan Ayyukan Raya Jihar

‎ ‎Majalisar Zartarwar Jihar Kano ta amince da kashe jimillar...

‎Gobara: Gwamnatin Kano ta tsaya tsayin daka don karbo alkawuran da aka yi wa yan kasuwar Singa – Rano

‎ ‎ ‎Gwamnatin jihar Kano ta ce tana iya bakin ƙoƙarinta...