Matar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, Asia Mohammad Ahmad, ta musanta ikirarin cewa Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II, na cikin mutanen da mijinta ke magana a kansu, bayan ya yi zargin cewa wasu abokansa da mutanen da ya taɓa taimakawa sun yi shiru a lokacin da yake fuskantar matsaloli.
Asia ta bayyana hakan ne a matsayin martani ga wani rubutu da Farfesa Farooq Kperogi ya wallafa mai taken “Sanusi and the Betrayal of El-Rufai”, inda ya yi hasashen cewa Sanusi II na iya kasancewa cikin mutanen da El-Rufai yake nufi.

Kperogi ya danganta hasashensa da tsohuwar alakar da ke tsakanin Sanusi II da El-Rufai, musamman irin goyon bayan da tsohon gwamnan ya bai wa Sanusi bayan gwamnatin Jihar Kano ta sauke shi daga sarautar Kano a shekarar 2020.
Sai dai Asia ta yi watsi da wannan hasashen, inda ta ce abin da Kperogi ya fahimta bai yi daidai da abin da su kansu suka sani ba.
Read also: 2023: Kwankwaso da Tinubu ba za su ci kano ba, ni zan kawo wa Atiku ita – Malam Shekarau
Read also: Masarautar Kano tana bayar da gagarumar Gudunmawa a bangaren Lafiya – Sarkin Kano
Read also: Rahoto: Matsin tattalin arziƙi na tilasta wa iyaye yi wa ‘ya’yansu auren wuri – UNICEF

Ta haka ne matar tsohon gwamnan ta musanta cewa mijinta yana nufin Sarkin Kano a cikin bayanan da ya yi game da mutanen da suka yi shiru a lokacin da yake cikin matsala.