Daga Rahama Umar Kwaru
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya sanar da sunaye manyan jami’an majalisar dattawa ta 10, wanda ya ce an samar da su ne hanyar masalaha .
Sabbin jami’an sun hada da Sanata Opeyemi Bamidele daga jihar Ekiti a matsayin shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa (Sanete Leader), Sanata Dave Umahi daga jihar Ebonyi a matsayin mataimakin shugaban masu rinjaye majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume daga jihar Borno a matsayin Mai tsawatarwa na majalisar, sai kuma Sanata Lola Ashiru daga jihar Kwara a matsayin mataimakiyar mai tsawatarwa.

A biyo mu sauran na nan tafe