‎Majalisar Zartarwar Kano Ta Amince Da Kashe Naira Biliyan 144 Kan Ayyukan Raya Jihar

Date:

‎
‎Majalisar Zartarwar Jihar Kano ta amince da kashe jimillar Naira biliyan 144 da miliyan 5 domin aiwatar da ayyukan raya jihar a fannoni daban-daban.
‎
‎An amince da kudaden ne a taron majalisar karo na 41 da aka gudanar ranar Alhamis, 24 ga Satumba, 2026, a Malam Aminu Kano House da ke Asokoro, Abuja.

IMG 20260704 WA0007
Talla

‎
‎Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Dr. Ibrahim Abdullahi Waiya, PhD, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a Kano.
‎
‎A cewarsa, ayyukan da aka amince da.kashe kudaden akan su sun shafi hanyoyi, ilimi, kiwon lafiya, samar da ruwa da makamashi, gidaje da sauran muhimman ayyukan more rayuwa.
‎
‎
‎Ma’aikatar Ayyuka ce ta samu mafi yawan kudaden, inda aka ware mata sama da Naira biliyan 84 da miliyan 975 domin aiwatar da ayyukan hanyoyi da gine-ginen gwamnati.
‎
‎Daga cikin hanyoyin da majalisar ta amince da ayyukansu akwai:
‎
‎- Rawul–Gani–Sitti–Masu–Gomo Road a Sumaila;
‎- Zaria Road–Gurjiya–Yankatsari–Rijiyar Gwangwan;
‎- Dawakin Kudu–Lahadin Makole Road;
‎- Da wasu hanyoyi a Nassarawa GRA, Tarauni, Kumbotso da Janbulo.
‎
‎A bangaren ilimi, majalisar ta amince da kashe sama da Naira biliyan 14 da miliyan 276, domin aiwatar da ayyukan da suka shafi bunkasa harkar ilimi a jihar.
‎
‎Haka kuma, an ware sama da Naira biliyan 2 da miliyan 608 ga bangaren kiwon lafiya domin gyaran cibiyoyin lafiya da inganta ayyukan asibitoci.
‎
‎Majalisar ta kuma amince da sama da Naira biliyan 11 domin ayyukan Ma’aikatar Filaye da Tsare-tsaren Birane, ciki har da samar da kayayyakin kula da zirga-zirga da inganta wasu muhimman ababen more rayuwa.
‎
‎Baya ga haka, Majalisar Zartarwar ta amince da kasafin kudin kari na shekarar 2026 na Naira tiriliyan 1 da biliyan 201, tare da umartar a mika kudirin ga Majalisar Dokokin Jihar Kano domin nazari da kuma amincewa.
‎
‎Majalisar ta kuma amince da gudanar da Kano Art and Cultural Festival (KANFEST) 2026, tare da amincewa da shirin hadin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu domin bunkasa Kano Energy and SME Industrial Park da ke Tamburawa.

FB IMG
‎
‎Haka kuma, majalisar ta umarci Ma’aikatar Ayyuka da ta duba hanyar Eastern Bypass zuwa Tsamiya Babba, Larabawar Abasawa da Nera Roundabout, domin tantance yiwuwar gudanar da aikin gyara a yankin.
‎
‎Taron majalisar ya gudana ne karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, inda aka tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban jihar da inganta rayuwar al’ummar Kano.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shin da gaske ne Sarki Sanusi ya ci amanar tsohon Gwamnan Kaduna? -Matar El-Rufai ta yi bayani

‎Matar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, Asia Mohammad...

‎Gobara: Gwamnatin Kano ta tsaya tsayin daka don karbo alkawuran da aka yi wa yan kasuwar Singa – Rano

‎ ‎ ‎Gwamnatin jihar Kano ta ce tana iya bakin ƙoƙarinta...

’Yan Kasuwar Singa Sun Nemi Gwamnatin Kano Ta Cika Alkawarin Tallafin Gobara

’Yan kasuwar Singa da ke birnin Kano, wadanda suka...

PDP ta sanya ranar sabon zaɓen fidda gwani a Gombe

Jam’iyyar PDP a Jihar Gombe ta tsayar da Talata,...