‎Mahaifiya ta kona ’yarta mai shekaru bakwai bisa zargin satar naman miya

Date:

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Anambra ta kama wata mata mai shekaru 32, Ogechi Ofoma, bisa zargin cin zarafi da jikkata ’yarta mai shekaru bakwai a yankin Ibollo da ke Awada-Obosi, Ƙaramar Hukumar Idemili ta Arewa a jihar.

‎An ce mahaifiyar ta jikkata yarinyar mai suna Oluebube da wukar da akan sanyata a wuta ta yi zafi, bayan zargin cewa ta ɗauki naman miya a cikin tukunya.

IMG 20260704 WA0007
Talla


‎Rahotanni sun ce ’yan sanda sun kama matar ne a ranar Lahadi, tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Harkokin Mata da Jin Daɗin Al’umma ta jihar.

‎A halin yanzu, ana tsare da wadda ake zargin a ofishin ’yan sanda na Awada, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

‎Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Anambra, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

‎Ya ce jami’an tsaro da wasu mazauna yankin ne suka taka muhimmiyar rawa wajen ceto yarinyar da kuma kama mahaifiyar.

‎Ikenga ya ce rundunar ta yi Allah-wadai da abin da ya faru, tare da tabbatar da cewa za ta tabbatar da an gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a lamarin a gaban doka.

‎A cewarsa, rundunar ta samu rahoton cin zarafin yarinyar ne a yammacin ranar 13 ga Satumba, 2026.

IMG 20260704 WA0005
Talla


‎Ya ce, “Matakin gaggawa da jami’an tsaro na yankin Ibollo, Awada-Obosi, tare da wasu mazauna yankin suka ɗauka, ya taimaka wajen ceto yarinyar da kuma kama mahaifiyarta, Mrs Ogechi Ofoma, mai shekaru 32.

‎“Bayanan binciken farko da aka samu sun nuna cewa an yi wa yarinyar mummunan rauni jiki, ciki har da raunukan da ake zargin an yi mata da wukar da ta dau zafi.”

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An fara sayar da hannun jarin matatar man Dangote

An buɗe hannun jari mafi girma a Afirka ga...

‎2027: Ya kamata gwamnatoci su rika samar da kariya ga yan jarida – Shugabar NAWOJ ta Kano

‎ ‎Ƙungiyar Mata ’Yan Jarida ta Ƙasa (NAWOJ), reshen Jihar...

‎ ‎Dan takarar gwamnan Kano a NDC ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa Ibrahim Khalil Danshagamu

Ɗan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar NDC, Comrade...