Abaya: Hukumar Hisba ta bayyana Matsayarta Dangane da Rigar Abaya

Date:

Daga Umar Ibrahim Sani Mainagge


Tun a kwanakin bayane wasu daga cikin matasa a jihar kano, suka dauki wata dabi’a tayin dan Kira ga duk budurwar data Sanya rigar abaya, hakan ta tilastawa ‘yan matan janye aniyarsu tayin yayin wannan Riga ta abaya a bikin Sallah karama data gabata.

Ko shakka babu wanana sara na ciwa ‘yan matan tuwo a kwarya tare da sakasu a cikin damuwa, Kuma haka ta tilastawa musu jibge wadannan riguna a gidajensu domin gujewa fadawa tarkon samarin kaga kenan abaya tazamewa ‘yan matan Dan zani Mai wuyar daurawa.

To sai dai Kuma a Wasu na cewa wannan Sara da samarin suka runguma hannu biyu-biyu tafara ciwa Hukumomi tuwo a kwarya, Hukumar nan mai hani da mummuna da Kuma umarnin da kyakkyawa wato Hukumar Hisba tafitar da matsayarta aka wannan sara tayin tozarci ga Yan Mata.


Ustaz Harun Muhammad sani ibni Sina shine babban kwamandan hisba na jihar kano yayi Kira ga samarin da su janye wannan aniyarsu tayin dan Kira ga ‘yan matan da suka sa rigar abaya domin kuwa riga da bata sabawa musulunci ba.

Sheikh Ibn Sina ya kuma Jan hankalin samarin dasu guji cin zarafin matune domin yin hakan ya sabawa addini Kuma ya sabawa Mutuntaka ta Dan adam .

Yace Hukumar su bazata lamunci Wannan mummunar dabi’ar ba , ya kuma bada tabbacin Hukumar zata saka Wanda guda da Duk Wanda aka Kama yaci zarafin Wata ‘ya mace data Sanya Abaya.

73 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kwamitin PTA na Kano ya dauki matakan hana ragewa dalibai hanya bayan taso su daga makaranta

DAGA ABDULHAMID ISAH Shugaban Kwamitin Iyayen yara da Malamai na...

Fada daba: Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf – Daga Zainab Nasir Ahmad

Daga Zainab Nasir Ahmad Mai Girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Abba...

RATTAWU ta Kano ta taya Abbas Ibrahim Murnar sabon mukamin da NUJ ta ba shi

Kungiyar ma'aikatan Radio da Talabijin ta kasa reshen jihar...

NUJ ta kasa ta baiwa Abbas Ibrahim sabon mukami

Daga Aliyu Abdullahi Danbala   Kungiyar yan Jarida ta Nigeria ta...