Ɗan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar NDC, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi kakkausar suka kan kisan gillar da aka yi wa wani mai sharhi kan al’amuran siyasa a kafafen sada zumunta, Ibrahim Khalil Dan Shagamu, a unguwar Gaida da ke ƙaramar hukumar Kumbotso ta jihar Kano.
Comrade Gwarzo ya bayyana kisan a matsayin abin mai matuƙar tayar da hankali da kuma ban tausayi, yana mai cewa lamarin ya kamata ya girgiza duk wani mai son zaman lafiya.

Ya ce bai kamata a halaka ɗan Adam saboda yana fadar ra’ayinsa ba, ya kamata a mutunta ra’ayin kowa tunda dokar kasa ta ba da dama kowa ya yi ra’ayin da yake ganin shi ya gamsu da shi.
A cikin wata sanarwa da kakakinsa, Ibrahim Garba Shuaibu, ya aikowa Kadaura24 ranar Alhamis a Kano, Gwarzo ya bayyana kisan a matsayin “mummunan aikin dabbanci kuma abin Allah-wadai ƙwarai.”
Ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta fara cikakken bincike domin gano hakikanin abin da ya faru, da kuma gano waɗanda suka aikata kisan tare da gurfanar da su a gaban kotu domin su fuskanci hukunci.
Rahotanni sun ce an kai wa Dan Shagamu hari tare da kashe shi a cikin gidansa da ke Gaida, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin damuwa tare da sake haifar da tambayoyi kan tsaron mutanen da ke amfani da kafafen sada zumunta wajen bayyana ra’ayoyinsu.
Gwarzo ya ce saɓanin ra’ayi, suka ko bambancin ra’ayin siyasa bai kamata ya zama dalilin kashe mutum ba.
Ɗan takarar gwamnan na NDC ya buƙaci hukumomin tsaro su bai wa lamarin muhimmancin da ya dace, yana mai gargadin cewa rashin hukunta waɗanda suka aikata kisan na iya ƙara haifar da fargaba tsakanin al’umma tare da rage amincewar jama’a ga tsarin tsaro.
Gwarzo ya kuma miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, abokansa da sauran makusantansa, yana roƙonsu da su kwantar da hankalinsu yayin da hukumomi ke gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Haka kuma, ya yi kira da a ƙara tsaurara matakan tsaro a sassa daban-daban na jihar Kano, yana mai jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyin jama’a na daga cikin muhimman nauyin da ya rataya a wuyan gwamnati.
Ya kuma shawarci mazauna jihar da kada su ɗauki doka a hannunsu ko kuma su nemi ɗaukar fansa, sai dai su bai wa hukumomin tsaro duk wani bayani da zai taimaka wajen gano tare da cafke waɗanda ke da hannu a kisan.