Ƙungiyar Mata ’Yan Jarida ta Ƙasa (NAWOJ), reshen Jihar Kano, ta kai ziyarar jajantawa ga shugabanni da ma’aikatan Gidan Rediyon Najeriya, Pyramid FM Kano, biyo bayan harin da wasu da ake zargin ’yan daba ne suka kai wa wasu ma’aikatan gidan rediyon.
An kai harin ne jim kaɗan bayan kammala taron jam’iyyar APC da aka gudanar a Jihar Kano, inda aka lalata tare da farfasa gilasan motar gidan rediyon.

Shugabar NAWOJ reshen Jihar Kano, Hajiya Bahijja Malam Kabara, ta ce ƙungiyar ta kai ziyarar ne domin jajantawa ’yan uwansu ’yan jarida tare da nuna rashin amincewarsu da harin da aka kai wa ma’aikatan gidan rediyon.
Hajiya Bahijja Kabara ta bayyana cewa ba za a lamunci wasu bata-gari su riƙa kai wa ’yan jarida hari ba, musamman a lokacin da suke gudanar da ayyukansu na aikin jarida ko kuma a kan hanyarsu ta dawowa daga wuraren ɗaukar rahotanni.
Ta yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike domin gano waɗanda suka aikata wannan aika-aikar, tare da tabbatar da cewa an hukunta su bisa tanadin doka.
Shugabar NAWOJ ta kuma yi kira ga shugabannin jam’iyyun siyasa da su ja kunnen magoya bayansu tare da tabbatar da cewa an kare ’yan jarida daga duk wani nau’in cin zarafi yayin da suke gudanar da ayyukansu.
Ta ce hakan ya fi muhimmanci musamman a wannan lokaci da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, wanda ake sa ran zai ƙara yawan ayyukan ’yan jarida wajen ɗaukar rahotannin tarukan siyasa da gangamin yaƙin neman zaɓe.
Ta bukaci gwamnatin jihar Kano ta dauki matakan baiwa yan jarida kariya yayin da suke gudanar da aiyukansu da dokar kasa ta tanada.
Hajiya Kabara ta ƙara jaddada buƙatar hukumomin tsaro a Kano su gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu, domin hakan ya zama darasi ga sauran masu irin wannan ɗabi’a.
Pyramid FM Ta Yi Godiya
Da yake mayar da jawabi, Mukaddashin Shugaban Gidan Rediyon Najeriya Pyramid FM Kano, Malam Umar Nuhu, ya bayyana farin cikinsa, a madadin shugabanni da ma’aikatan gidan rediyon, bisa ziyarar jajantawar da shugabannin NAWOJ suka kai musu.
Malam Umar Nuhu ya bayyana godiya ga ƙungiyar NAWOJ, yana mai cewa irin wannan lamari ba zai karya wa ma’aikatan gidan rediyon gwiwa ba, sai dai ya ƙara musu ƙwarin gwiwar ci gaba da gudanar da aikinsu.
Ya ce ma’aikatan Pyramid FM za su ci gaba da gudanar da aikin jarida cikin ƙwarewa, gaskiya da adalci, musamman wajen ɗaukar rahotannin harkokin siyasa da sauran abubuwan da suka shafi rayuwar al’umma.

Ya kuma jaddada cewa, duk da kalubalen da ka iya tasowa a yayin gudanar da ayyukan jarida, gidan rediyon zai ci gaba da tsayawa kan ƙa’idodin aikin jarida tare da bai wa jama’a sahihan bayanai.
Malam Umar Nuhu ya ce wannan matsaya ta ƙara zama wajibi ne yayin da Najeriya ke tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.