‎ ‎2027:Jam’iyyar NDC za ta nemi gudunmawar kudi daga yan Najeriya don gudanar da yakin neman zabenta

Date:

Jam’iyyar adawa ta NDC ta ce za ta nemi gudunmawar kudi daga talakawan Najeriya domin gudanar da yakin neman zabenta a zaben 2027.

‎Uban jam’iyyar na kasa, Sanata Seriake Dickson ne ya bayyana haka yayin wata hira da gidan talabijin na Arise News a ranar Laraba.

IMG 20260704 WA0007
Talla


‎Sanata Dickson, wanda ke wakiltar Bayelsa ta Yamma a Majalisar Dattawa, ya ce NDC ce jam’iyyar siyasa daya tilo a Najeriya da ba ta samun kudin gudanar da ayyukanta daga baitul malin gwamnati.

‎Ya ce jam’iyyar na shirin bai wa yan Najeriya damar bayar da gudunmawa daga Naira 1,000 zuwa Naira 2,000 domin taimakawa wajen gudanar da ayyukanta da yakin neman zabenta.

‎“Ba za a bar dimokuradiyyarmu ta dogara da kudin attajirai da biliyoyin kudi na gwamnati ba,” in ji Sanata Dickson.

IMG 20260704 WA0005
Talla


‎Ya kuma ce jam’iyyar na tuntubar masu ruwa da tsaki kan wadanda za su kasance cikin kwamitin yakin neman zabenta na shugaban kasa, yana mai cewa za a sanar da sunayensu nan ba da jimawa ba.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

‎2027: Ya kamata gwamnatoci su rika samar da kariya ga yan jarida – Shugabar NAWOJ ta Kano

‎ ‎Ƙungiyar Mata ’Yan Jarida ta Ƙasa (NAWOJ), reshen Jihar...

‎ ‎Dan takarar gwamnan Kano a NDC ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa Ibrahim Khalil Danshagamu

Ɗan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar NDC, Comrade...

Ƴansanda a Kano sun kama mutane 2 da ake zargi da hannu a kisan Ibrahim Khalil Ɗanshagamu

 Rundunar ƴansandan Jihar Kano ta ce ta kama wasu...

Kwankwaso ya magantu kan Kisan Ibrahim Khalil Danshagamu

Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na Jam’iyyar NDC, Sanata...