Sojoji sun kashe yan Bindiga 19 a Kano

Date:

Sojojin Najeriya sun ce sun samu nasarar daƙile ƴanbindiga daga yunƙurin da suka yi na kai hari a wasu ƙauyuka na ƙaramar hukumar Shanono ta jihar Kano.

Sojojin na aikin soji na musamman na MESA da ke ƙarƙashin birged na uku da ke Kano ne suka yi jagoranci aikin bayan bayanan sirri da suka ce sun samu kan yunƙurin ƴanbindigar na kai harin.

InShot 20250309 102512486

A wata sanarwa da kakakin sashen, Babatunde Zubairu ya fitar, ya ce, “mun samu bayanan sirri ne cewa an ga ƴanbindiga a ƙauyen Unguwan Tudu da Unguwar Tsamiya da Goron Dutse a ƙaramar hukumar Shanono da misalin ƙarfe biyar na yamma a ranar 1 ga watan Nuwamba.”

Ya ce wannan ne ya sa aka tura sojoji yankin domin fuskantar maharan, “inda suka samu nasarar tarwatsa su bayan musayar wuta da aka yi na tsawon lokaci.”

“Haka kuma sojojin da aka tura ƙauyen Tsaure sun gamu da ƴanbindiga, inda nan suka yi musayar wuta, har suka kora su, sannan suka ƙwato babura da makamai.”

Sanarwar ta ce sojoji sun kashe ƴanbindiga 19 a gumurzun, “amma an kashe mana sojoji guda biyu,” in ji shi.

Kwamandan sashen Birgediya Janar Ahmed Tukur ya buƙaci mutanen yankin su ci gaba da gudanar da harkokinsu, sannan ya yi kira gare su da su riƙa sa ido kan abubuwan da ke wakana tare da kai musu bayani da gaggawa.

Ya kuma yi alƙawarin haɗa hannu da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da tsaro a jihar Kano baki ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...