Gwamnatin Jihar Kano ta ce ba za ta yi watsi da matasan da suka tuba daga harkar daba ba, domin tana ganin akwai baiwar da suke da ita wadda za ta amfanar da al’umma idan aka taimaka musu da irin kulawar da ta dace.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan a wani taro da aka shirya domin karɓar wasu matasa da suka yanke shawarar barin harkar daba.
Waiya ya ce matasan da suka rayu a cikin wannan hali na da wasu fasahohi da za su iya amfani ga jihar, musamman idan aka dawo da su cikin al’umma aka kuma ba su damar gyara rayuwarsu.

Ya ce saboda haka ne gwamnati ta samar da shirin yin afuwa domin tsamo matasan da ke harkar daba tare da tabbatar da cewa zaman lafiya ya ci gaba da dorewa a Jihar Kano.
Kwamishinan ya bayyana cewa zuwa yanzu an tantance matasa 1,654 da aka saka cikin shirin Safe Corridor, kuma nan gaba za a ci gaba da tantance wasu matasa 2,100 domin su ma su shiga cikin shirin. Ya ce bayan kammala wannan matakai, za a mika su gaban gwamna domin karɓar tallafin da zai taimaka musu wajen dogaro da kansu.
Ya ce babban manufar shirin ita ce ganin matasan sun ajiye makamansu, su kuma dawo cikin al’umma domin su zamo masu amfani maimakon zama barazana ga zaman lafiya.
Fadar shugaban kasa ta yaba wa Kwankwaso bisa martanin da ya yi wa Trump kan barazana ga Najeriya
Waiya ya tabbatar da cewa gwamnatin Jihar Kano, karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, za ta ci gaba da tallafawa dukkan matasan da suka nuna shirye-shiryen barin dabi’un tashin hankali don su samu ingantacciyar rayuwa.
Da yake nasa jawabin Dan Amar din Kano Alhaji Aliyu Harazimi ya bukaci Matasan da su dage wajen tsayar da sallah domin yin Sallar yana kawar da mutane daga aikata abubun da basu dace ba.
Ya bukaci mawadata da sauran Shugabanni da su shigo cikin Shirin domin tallafawa yunkurin gwamnatin Kano na kawar da harkar daba a jihar Kano baki daya.