Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa
Shugaban karamar hukumar Rano malam muhd Naziru ya’u ya yi alkawarin yin duk mai yiwuwa don ganin abun da ya faru a karamar hukumar bai sake faruwa ba.
” Tabbas mun yi takaicin abun da ya faru jiya ( Litinin) a karamar hukumar Rano, amma mun fara daukar matakan da suka dace domin ganin hakan ba ta sake faruwa ba a nan gaba”.

Shugaban karamar hukumar ta Rano ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a Kano.
Ya ce abubuwan da duka bangarorin guda biyu suka yi ba haka ya kamata ace sun yi ba, amma abun da ya faru ya riga ya faru kuma muna fatan hakan ba zai sake faruwa ba.
Sarkin Musulmi ya umarci yan Nigeria su fara duban watan Zulhijja
Malam Muhd Naziru ya yi kira ga al’ummar yankin musamman matasa da su guji daukar doka a hannu .Ya kuma bukaci al’ummar karamar hukumar da su kwantar da hankulansu komai yaci gaba da guda na ba tare da wata fargaba ba.
Ya ce yanzu haka tuni sauran Jami’an tsaro su ka dukufa domin ganin sun lalubo bata garin da suka kawo tashin hankali a karamar hukumar Rano.
Ya ce da zarar gwamna Abba kabir yusif ya dawo daga tafiyar da ya yi za su sanar da shi tare da ba shi cikakken rahoton musabbin mutuwar matashi Abdullahi musa da kuma na mutuwar babban baturen yan sandan karamar hukumar ta Rano.
ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalai da yan uwan Abdullahi Musa da na matashin da ya rasa ransa, haka zalika ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalai da kumar al’ummar jihar Nasarawa bisa rasuwar baturan yansanda na karamar hukumar Rano Baba Ali wanda Dan asalin jihar ta Nasarawa ne