Hukumomi a kasar saudiyya sun tabbatar da ganin jinjirin watan Zulhijja na shekara ta 2025.
Shafin Haramain Sharifain ne ya tabbatar da hakan yau talata.

Sanarwar ta ce wannan na nufin gobe Laraba ita ce daya ga watan Zul-Hijja 1446 bayan hijira.
Ranar Alhamis 5 ga watan Yuni ita ce ranar Arfa, yayin da za a hau idin babbar sallah a ranar Juma’a 6 ga Yuni.