Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Mai martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya sanar da rundunar ‘yan sandan jihar Kano shirin sa na gudanar da hawan Sallah karama .
A wata wasika da jaridar Kadaura24 ta gani, Sakataren Sarkin Abdullahi Haruna Kwaru ne ya sanar da kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano da Hukumar DSS da ta Civil defense cewa Sarkin ya kammala shirye-shiryen gudanar da bikin, wanda zai gudana a karshen watan Maris na 2025.

Kamar yadda wasikar ta nuna, za a gudanar da bukukuwan Hawan Sallar Idi, da Hawan Daushe, da Hawan Nassarawa a ranakun 1, 2, da 3 ga watan Shawwal 1446, sannan a yi bikin al’adu a rana ta hudu.
Wasikar ta Kwaru ta nuna cewa, a bana za su hade bikin cikar Sarkin shekaru biyar a kan karagar magabatansa.
“Makasudin wannan wasiƙar ita ce sanar da hukumomin tsaro a Jihar Kano, musamman rundunar ‘yan sanda a hukumance, cewa bikin Sallah na bana ya zo daidai da cika shekaru biyar (5) da Mai Martaba ya yi a kan karagar mulkin magabatansa, tare da ba da tabbacin cewa za a gudanar da dukkan bukukuwan cikin lumana.” a cewar wasikar.
2027: Shekarau ya Caccaki hadakar Atiku da El-Rufai da Obi
Ya bayyana fatan a gudanar da bukukuwan lami lafiya tare da addu’ar neman kariya, koshin lafiya, da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Ofishin Sarkin ya nemi hadin kan hukumomin tsaro don tabbatar da an gudanar da bukukuwan kwanciya hankali da lumana kuma cikin nasara.
Haka kuma a wata sanarwa da sakataren yada labaran Sarkin Abubakar Balarabe kofar Na’isa ya fitar ya bukaci al’ummar Musulmi da su fita domin ganin yadda Sarkin za gudanar da bukukuwan sallah karama.