Kyautata dabi’u shi ne zai kara kusanta al’umma da Allah – Ustaz Tijjani Isma’il

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Wani malamin addinin musulunci a Kano mai sunan Ustaz Tijjani Sheikh Isma’il Khalifa ya ce akwai bukatar al’ummar Musulmi su sake kyautata dabi’unsu kamar da yadda su ke yin Ibada .

” Wani bincike ya nuna cewa yan Nigeria su ne na biyu wajen yin Ibada, amma abin takaici kuma su ne a gaba wajen cin hanci da rashawa da aika abubuwan da na su dace ba”

Ustaz Tijjani Sheikh Isma’il Khalifa ya bayyana hakan ne yayi da yake gabatar da lacca a zawiyatu ahlul faidatu Tijjaniyya dake gidan Alhaji Uba Ibrahim Ringim a Kano.

InShot 20250309 102403344
Talla

Ya ce da yadda al’ummar Nigeria ke maida hankali a sha’anin ibada haka su ke maida hankali wajen kyautata dabi’unsu da an sami saukin halin da ake ciki a kasar.

“Kyawawan halaye su suke inganta rayuwar al’umma, kuma su ya kamata Shugabanni da mabiya a Nigeria su kyautata don gyaran matsalolin da kasar ta ke ciki”.Inji Ustaz Tijjani Sheikh Isma’il Khalifa

2027: Shekarau ya Caccaki hadakar Atiku da El-Rufai da Obi

“Duk wanda yake yawan ibada kuma yana cutar mutane ta hanyar yin ha’inci a kasuwa ko a ofis ko ma ta Kowacce fuska to ya je ya sake duba ibadar sa , domin duk wanda Allah ya ke karbar ibadunsa to za ka ganshi da kyawawan halaye”.

Ya ce duk masu burin ganin kasashen Amuruka da burtaniya da Faransa sun ruguje, su ma daina, saboda su sun yarda da kyautata dabi’unsu da yin adalci ga al’ummarsu.

Ustaz Tijjani Sheikh Isma’il Khalifa ya bukaci al’ummar Musulmi da su mai da hankali wajen kyautata dabi’unsu da mu’amalarsu da sauran mutane domin haduwa da Allah salin alin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...

Tinubu ka fadawa yan Nigeria Inda ka tsaya har kwana 5 bayan taron BRICS – ADC

    Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC ta soki Shugaban...

Da dumi-dumi: Yadda akai Jami’an tsaro suka kama ni -Danbello

Rahotannin sun tabbatar da cewa jami'an tsaro a Nigeria...