Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jagoranci rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim.
Da aka rantsar da sabon Sakataren a ofishinsa, gwamna Abba Kabir Yusuf ya hore shi da ya gudanar da ayyukansa bisa gaskiya da rikon amana tare da sadaukar da kai a yayin aikinsa.

Ya bayyana kwarin gwiwarsa akan sabon Sakataren gwamnatin, tare da fatan zai yi amfani da gogewarsa wajen tabbatar da kudirin gwamnatin jiha na aiwatar da ayyukan cigaba da bunkasa rayuwar al’ummar jihar Kano.
Inganta Ilimi: Abba Bichi ya dauki sabbin malamai 200 aiki
Kadaura24 ta rawaito cewa a nasa bangaren, sabon Sakataren gwamnatin jiha, Alhaji Umar Farouk Ibrahim ya yi alwashin zai bada gudunmawarsa domin daga darajar jihar Kano zuwa mataki na gaba.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito cewa a ranar asabar gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bayar da sanarwar nada Farouk Umar Ibrahim a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar Kano.