Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bukaci masu magana a gidajen radio a Kano musamman wadanda suke jam’iyyun adawa da su rika yin adawa mai ma’ana cikin mutunci da girmamawa.
Kwamared Waiya ya bayyana hakan ne lokacin da ya gana da masu magana a gidajen radio cikinsu har da yan jam’iyyun adawa.

A yayin taron, Waiya ya bayyana jin dadinsa da ganin wakilai daga jam’iyyun siyasa daban-daban da suka halarci taron. Inda ya bayyana zuwan su da cewa kishin jihar Kano ne ya kawo, domin da ba sa kishin da ba za su je wajen taron ba.
Da yake jaddada mahimmancin adawar siyasa, Waiya ya ce duk da bambance-bambancen Jam’iyya, amma ya kamata a rika mutunta juna ta hanyar kaucewa kalaman da masu dace ba.
Gwamna Abba ya Rantsar da Sabon Sakataren Gwamnatin Kano
A wani bangare na kudurin sa na inganta harkokin siyasa, kwamishinan ya sake jaddada shirinsa na farfado da kungiyar nan ta Gauta Club, kungiyar da ta hada kan masu magana a gidajen radio a baya ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ko ra’ayi ba.
Ya kara da cewa kungiyar ta Gauta ta taka muhimmiyar rawa a baya wajen saita al’amuran masu magana a gidajen radio, inda ‘yan kungiyar suka rika tattaunawa da juna tare da mutunta juna, ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba.
Da yake jawabi tun da farko, Shugaban kungiyar Gauta a Jihar Kano, Alhaji Hamisu Danwawu Fagge ya yabawa Kwamishinan bisa kiran taron ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba.
Ya bayyana kokarin kwamishinan na ganin an tsaftace harkar magana a gidajen radio a matsayin wani abun alfahari da za su baiwa goyon baya don cigaban jihar Kano.