Daga Abubakar Lawan Bichi
Gidauniyar Marigayi Kabir Abubakar Bichi Karkashin Kulawar Dan Majalisar tarraye Hon. Abubakar Kabir Abubakar ta dauki Sabbin Malamai Makaranta 200.
Adadin Malaman dake karkashin Gidauniyar yanzu ya kai har kimanin 318.
Malaman za su koyar a makarantun Firamare da Sakandire da kuma islamiyyoyi dake fadin Karamar Hukumar Bichi.

Tunda farko a shekarar 2020 kwamatin ilimi na Dan Majalissar Tarayya ya dauki ma’aikatan koyarwa har mutum 106 wadanda suke koyarwa a makarantun firamare a fadin Karamar Hukumar Bichi inda daga farko yawansu ya koma 118.
A wata taran daya gabatar Dan majalissar tarayya Hon. (Dr.) Abubakar Kabir Abubakar ya yi musu karin albashi daga N18,000 zuwa N60,000 (333% increment).
Tinubu ya ba da umarnin a baiwa Kwankwaso, Bichi da sauran wadanda ya nada takardun kama aiki
A ranar 10 ga watan October, 2024, Hon. (Dr.) Abubakar Kabir Abubakar ya bada umarnin sake daukar sababbin malamai na makaranta mutum 200 nan take domin kara samarda malamai masu hazaka dubada yanayin karancin Malamai da ake fama dashi a Karamar hukumar Bichi.
A dauki Malaman Islamiyya 50 (Maza 42, Mata 8) Sai Makarantun Primary a dauki 130 (Maza 64, Mata 66) da kima Upper Basic mutum 98 (Maza 63, Mata 35).
Sai kuma Senior Secondary School a dauki malamai 40 (Maza 27, Mata 13)
Gaba daya jimlar Ma’aikatan ta kama 318 kenan. Maza 196, Mata 122.
Kowanne wata Dan Majalissar Tarayya zai biyasu albashi Naira miliyan sha tara da dubu tamanin (N19,080,000).