Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata Barau Jibrin ya bayyana kudirnsa na tallafawa matasa 558 da suka fito daga yankin arewa maso yammacin Nigeria da tallafin Naira Biliyan 2 don inganta harkokin noma a yankin.
Sanata Barau Jibrin ya zai ba da tallafin ne a karkashin wani shiri mai taken: Barau Initiative for Agricultural Revolution in the North West (BIARN), za a zabo matasa manoma uku daga kowace kananan hukumomi 186 na jihohi bakwai da suka kunshi shiyyar Arewa maso da suka haɗar da Kano, Kaduna, Katsina, Kebbi, Jigawa, Sokoto da Zamfara.
![InShot_20250115_195118875 InShot 20250115 195118875](https://kadaura24.com/wp-content/uploads/2025/01/InShot_20250115_195118875-300x298.png)
Ya ce duk wanda ya yi nasara a shirin zai samu Naira miliyan 5 don yin noma a wannan kakar, kuma kimanin Naira biliyan 2.79 za a raba wa matasan da suka yi nasara.
Sanata Barau, ya ce an kirkiri wannan shiri ne domin bunƙasa harkar noma domin samun wadatar abinci kamar yadda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da sabon tsarin haɓaka noma don samar da abinci.