Majalisar wakilci ta dauki matakin don magance tsadar kayan abinchi a Nigeria

Date:

Daga Ibrahim Dahiru Ahmad

 

Mambobin Majalisar Wakilai sun amince a zaftare rabin albashinsu na tsawon watanni shida saboda yunwa da tsadar rayuwa da ake fama da ita a Najeria.

’Yan Majalisar sun yi ittifakin yanke rabin albashin nasu ne bayan bukatar hakan da Mayaimakin Shugaban Majalisar, Benjamin Okezie Kalu, ya bagatar.

Talla

Benjamin Okezie ya nemi kowane dan majalisar ya hakura da rabin tsurar albashinsa na N600,000 a kowane wata domin tallafa wa ’yan Nijeriya da ke cikin halin matsin rayuwar a halin yanzu.

Mataimakin shugaban majalisar ya ce za a yi amfani da albasin nasu da aka yanke ne wajen taimaka wa gwamnati don magance tsadar kayan amsaraufi domin kawo saukin lamurra ga al’ummar kasar.

Sabbin Sarakunan Rano da Karaye sun ziyarci Sarki Sanusi II

Kalu ya gabatar da wannan bukata ne a kan rokon da Honorabul Isiaka Ayokunle ya yi ga masu shirin gudanar da zanga-zangar gama-gari kan tsadar rayuwa, cewa su janye su hau teburin tattaunawa da gwamnati.

Da wannan yanke rabin albashi da ’yan majalisar su 360 suka yi, a duk wata za su hakura da jimillar kudi Naira miliyan 108.

A tsawon watanni shida kuma, jimillar abin da za a yanke musu shi ne Naira miliyan 648.

Majalisar ta amince da kudurin kuma ta aike da shi ga kwamitin kasafi kudade da ayyukan jin kai domin aiwatar da yanke albashin mambobin.

Daily Trust

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Majalisar Dokokin Kano ta yi Doka kan masu tufar da yawu da majina a titi

Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da dokar cin...

Sanata Barau zai baiwa dalibai 1,000 tallafin karatu a Kano ta tsakiya da ta Kudu

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau...

Kamfanin Gerawa ya ba da tallafin Kwamfutoci 100 ga al’ummar Gezawa

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa   Kamfanin shinkafa na Gerawa Rice Mills...

Gwamnan Kano ya baiwa maja-baƙin Sheikh Karibullah da wasu malamai muƙami

    Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...