Za mu Cikawa Daliban Kano Burinsu – Gwamnatin Kano

Date:

Daga Isah Ahmad Getso

 

Mai baiwa gwamnan jihar Kano shawara kan harkokin dalibai Nura Iro ma’aji ya ba da tabbacin gwamnatin Kano za ta yi amfani da shawarwarin da daliban jihar suka bata wajen inganta harkokin ilimi.

” Mun ji korafe-korafe da shawarwarin ku Kuma za mu mikawa gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf domin yin nazari akansu da kuma aiki da su don inganta harkokin ilimi kamar yadda ya faro”

Nura Iron ma’aji ya bayyana hakan ne Yayin taron karbar korafe-korafe da shawarwari daga daliban jihar kano kan yadda za a inganta ilimi, wanda ya gudana a gidan mumbayya House.

Talla

Ya kara da cewa gwamnan kano a shirye yake daya ci gaba da baiwa bangaren ilimin kulawar da ta dace, a kokarinsa na magance dumbin matsalolin da ilimi yake fuskanta a fadin jihar .

Sabbin Sarakunan Rano da Karaye sun ziyarci Sarki Sanusi II

Ya ba da tabbacin gwamnatin jihar kano zata kara bunkasa harkokin zaɓen shugabannin Kungiyoyin dakibai na jihar da na kasa baki daya.

Musa Iliyasu Kwankwaso ya soki gwamnatin Kano kan sabbin masarautu masu daraja ta biyu

” Mun fuskanci akwai matsaloli a yadda kuke gudanar da zubukanku , don haka za mu dauki matakan da suka dace don ganin kun shirya sabon zabe, tun da har kun kwashe kimanin Shekaru 8 baku gudanar da zabe ba, wanda kuma hakan ya sabawa dimokaradiyya”.

Daga karshe Yaja hankalin daliban da su maida hankali wajen karatunsu, don cin moriyarsa a nan gaba .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ta ɗaure wani ɗan Tiktok mai wanka a tsakiyar titunan Kano

    Wata kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya...

Damuna: Mun shirya inganta wuraren tsayarwar motocinmu – Kungiyoyin Direbobin na Kano

Kungiyar matuka motocin kurkura ta jihar Kano da Kungiyar...

Rasuwar Aminu Ɗantata babban rashi ne ba ga Nigeria kadai ba – Mustapha Bakwana

Daga Zakaria Adam Jigirya   Tsohon Mai baiwa gwamnan Kano shawarawa...

Gwamnatin Kano ta yabawa Tinubu saboda gyarawa da bude NCC DIGITAL PARK

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin jihar Kano ta yabawa Gwamnatin...