Daga Rahama Umar sagagi
Gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu a sabuwar dokar da ta samar da karin masarautu masu daraja ta biyu a jihar.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa a yau talata majalisar dokokin jihar kano ta amince da kudirin dokar da ta samar da karin masarautun masu daraja ta biyu.
Gwamnan ya sanya hannun ne a yammacin yau talata a gidan gwamnatin jihar kano.
Da dumi-dumi: Majalisar dokokin jihar kano ta kirkiri sabbin masarautu
Gwamnan ya sanya hannu kan kudirin bayan majalisar dokokin jihar ta amince da shi ya zama doka .
Sabbin Masarautun masu daraja ta biyu sun hadar da: Rano, Karaye da Gaya.