Rikicin Masarautu: Mataimakin Gwamnan Kano ya nemi Afuwar Nuhu Ribado

Date:

Mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamaret Aminu Abdussalam Gwarzo Kano ta ba wa Mashawarcin Shugaban Kasa kan sha’anin Tsaro Nuhu Ribadu hakuri kan zargin sa hannunsa a rikicin masarautun jihar.

Kadaura24 ta ruwaito mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdulsalam a ranar Asabar yana zargi Ribadu da yunkurin dawo da Alhaji Aminu Ado Bayero kan kujerar Sarkin Kano bayan gwamnatin jihar ta sauke shi tare da sauran sarakunan jihar.

Zanga-zangar goyon bayan Aminu Ado Bayero ta barke a Kano

Daga bisani Ribadu ya nesanta kansa da kuma ofishinsa daga rikicin, sannan ya yi barazanar maka mataimakin gwamnan a kotu.

Mataimakin gwamnan ya baiwa Ribadon hakuri ne yayin wani taron manema labarai a daren jiya Lahadi.

Bayan haka ne mataimakin gwamnan ya ba da hakuri ga Ribadu yana mai cewa yaudarar gwamnatin aka yi da bayanan da aka ba .

Gaskiyar Lamari Kan Halin Da Ake Ciki a Masarautar Kano

” Don haka yanzu a madadin ni kai na da gwamnatin jihar kano Muna baiwa mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro hakuri, kuma muna bashi tabbacin za mu cigaba da ba shi hadin kai da goyon baya don ya gudanar da aikin sa yadda ya kamata”. Aminu Abdussalam Gwarzo

“Mun kara zurfafa bincike inda kuma gano cewa yaudarar mu aka yi, saboda haka, a madadin gwamnatin Kano, mana ba da hakuri ga Mashawarcin Shugaban Kasa kan Sha’anin Tsaro,” in ji mataimakin gwamnan.

Gwamnatin jihar ta kuma bukaci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya baki kada abin ya kara rincabewa fiye da haka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Jam’iyyar APC ta Fadi Matsayarta Kan Sulhunta Kwankwaso da Ganduje

Jam'iyyar APC ta jihar Kano ta ce kokarin shigowa...

Tiktok ya ayyana ranar daina aiki a kasar Amuruka

TikTok ya bayyana cewa zai 'daina aiki' a Amurka...

Kwamishina Waiya ya karbi bakuncin Shugabannin Jaridar Daily trust

Daga Aisha Muhammad Adam   Kwamishinan yada labarai na jihar Kano...

Tallafin N30m: EFCC da hukumar yaki da rashawa ta Kano sun karbi korafi kan wasu hadiman gwamnatin Kano

Wasu ya'yan kungiyar NNPP Kwankwasiyya Media Forum sun kai...