Yanzu-yanzu: Jam’iyyar APC ta Fadi Matsayarta Kan Sulhunta Kwankwaso da Ganduje

Date:

Jam’iyyar APC ta jihar Kano ta ce kokarin shigowa APC Kwankwaso yake yi shi ne Dalilin sa ya Abdulmumin Jibrin Kofa ya fara kiraye-kirayen a sami sulhu tsakanin Kwankwaso da Ganduje.

β€œMaganar sulhu tsakanin Kwankwaso da Ganduje da Kofa yazo da ita yaudara ce, a siyasance ba ma buΖ™atar yin siyasa tare da Kwankwaso”.

Kadaura24 ta rawaito mai magana da yawun Jam’iyyar APC reshen jihar Kano Ahmad S Aruwa ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da ya yayi da Hikima Radio dake Kano.

InShot 20250115 195118875
Talla

” So suke so dawo APC don su kwace ta daga wajenmu, domin Kwankwaso ya saba yin hakan tun da ya yiwa Malam Ibrahim Shekarau Wanda ta dole sai da muka bar masa APC muka koma PDP, haka kuma ya sake yi mana a PDPn don haka mun gano wayon”. Inji Kakakin APC

Ya ce idan da gaske ke gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ne ya kamata ya dai-data Kwankwaso da Ganduje, amma ba Kofa ba.

Da dumi-dumi: Baffa Babba ya yiwa Kofa Martani Kan sulhunta Kwankwaso da Ganduje

” Idan ka lura da yadda Kofa ya tsayyano mukaman da Kwankwaso ya rike da wadanda Ganduje ya rike zaka gane shi (Kofa) ya yi kankanta ya ce zai sulhunta Kwankwaso da Ganduje”. A cewar Aruwa

Kakakin APC reshen jihar Kano ya ce su ba sa bukatar yin sulhu tsakanin Kwankwaso da Ganduje saboda a cewarsa daga karshe cewa za ayi a hade, kuma in an hade su za a cutar.

Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji Abdulmumin Jibrin Kofa a karshen makon da muke bankwana da shi , ya ce ya sama wajibi a sulhunta Ganduje da Kwankwaso saboda cigaban jihar Kano

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related