Tiktok ya ayyana ranar daina aiki a kasar Amuruka

Date:

TikTok ya bayyana cewa zai ‘daina aiki’ a Amurka daga ranar Lahadi, matuƙar dai gwamnatin shugaba Joe Biden ba ta ɗauki matakin hana dakatar da shi ba.

Hakan na zuwa ne bayan Kotun ƙolin ƙasar, a ranar Juma’a ta amince da matakin Majalisar dokokin Amurka na haramta ayyukan manhajar, har sai idan kamfanin da ya mallaki manhajar – wanda ke da alaƙa da China – ya amince zai sayar da ita ga wani kamfanin Amurka, bisa dalilai na tsaro.

InShot 20250115 195118875
Talla

Fadar shugaban Amurka ta White House ta ce ba za ta bayar da umarnin amfani da dokar ba, to amma TikTok ya ce idan har da gaske ne to ya kamata gwamnati ta fitar da sanarwa domin tabbatar wa kamfanonin Apple da Google matsayar tata.

Kwamishina Waiya ya karbi bakuncin Shugabannin Jaridar Daily trust

Donald Trump, wanda za a rantsar a matsayin shugaban Amurka a ranar Litinin – ya nuna aniyar ganin ba a tabbatar da haramcin amfani da mahajar ba.

Majalisar Dokokin Amurka ce ta yanke shawarar haramta TikTok a ƙasar ne bisa dalilai na tsaro, inda ta ce akwai yiwuwar gwamnatin China na amfani da mahajar wajen tattara bayanan mutanen Amurka, wanda take amfani da shi wajen yaɗa manufa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...