Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Shugaban hukumar ingantuwar aiyuka ta Kasa Baffa Babba Danagundi ya ce yana goyon bayan kalaman da dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji Abdulmumin Jibrin Kofa ya yi na nema a sulhunta Ganduje da Kwankwaso.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito Abdulmumin Jibrin Kofa ya ce ya zama dole su sulhunta Ganduje da Kwankwaso domin cigaban jihar Kano.
Baffa Danagundi ya ce batun da kofa ya zo da shi, batu ne da ya kamata a marasa masa baya domin cigaban jihar Kano.

Sai dai ya ce akwai bukatar a fadada batun a hada da Shekarau da Kabiru Gaya domin su ma tsofaffin gwamnoni ne da suke da gudunmawar da za su bayar wajen cigaban jihar Kano.
Dangote ya kara farashin man fetur a Nigeria
” Tabbas duk wani mai kishin cigaban Kano dole ya goyi bayan wannan batu na Kofa, Muna goyon bayanka kuma za mu baka duk wani goyon baya domin tabbatar da wannan sulhu tsakanin Kwankwaso da Ganduje da Shekarau da Kabiru Gaya”. Inji Baffa Babba
Baffa Babba Danagundi ya ce ya yi mamakin yadda gwamnan Kano ya dauko batun samar da majalisar tsofaffin gwamnonin Kano domin a rika tattaunawa don cigaban jihar Kano, amma ya fasa.