Ɗan majalisar tarayya na Wudil da Garko ya ƙaddamar da bada tallafi ga kimanin mutane ɗari Uku

Date:

Daga Muhammad Rano

 

Kimanin mutum 300 ne suka amfana da tallafin sha ka tafi wanda ɗan majilisar tarayya mai wakiltar Wudil da Garko ya ƙaddamar.

 

Tallafin na zuwa ne a dai dai lokacin da al’umma ke cikin kunci da matsin rayuwa tun bayan da gwamnatin tarayya ta amince da cire tallafin man fetur.

 

Ɗan majalisar tarayyar Hon. Abdulhakeem Kamilu Ado, ya ƙaddamar da tsarin na sha ka tafi da zai dinga zaƙulo maban bantan mutane daga sassan ƙananan hukumomin biyu a duk ƙarshen wata domin basu tallafin dubu biyar (₦5000) domin amfanin yau da kullum.

Talla

Shirin sha ka tafi wani tsari ne da mahaifin ɗan majalisar marigayi Alhaji Kamilu Ado Isa Ajiyan Makama ya fito dashi a lokacin da ya jagoranci ƙaramar hukumar Wudil a tsakanin shekarun 1999-2003.

Tinubu ya sake tura tawagar Malamai zuwa Jamhoriyyar Nijar

Da yake jawabi yayin ƙaddamar da bada tallafin Hon. Abdulhakeem Kamilu Ado, cewa yayi ” mun zaɓi dawo da wannan tsari ne tun bayan tsawon shekaru (kamar yanda wani makaho ya bani labarin cewa; sun manta irin wannan a rayuwarsu); duba da yanayin wahalar rayuwa da ake ciki.

Bai Kamata Gwamnatin Kano ta yi Auren Zawarawa a Wannan Lokacin ba – Shitu Sani Marshall

”A don haka muka ƙaddamar da waɗanda zasu gabatar da irin wannan tallafi su kimanin mutum 40 da suma zamuna boyansu albashi duk wata domin zaƙulo mutanen da su ka can-canta daga mazaɓunmu na ƙananan hukumomin Garko da Wudil, ta hanyar bibiyar mutanen (maza da mata) 300 har garuruwansu domin basu wannan tallafi”.

A yayin taron dai ɗan majalisar ya jagoranci aza tubalin ƙaddamar da sanya fitilu masu amfani da hasken rana wato (Solar light) a wasu sassa na ƙaramar hukumar Wudil tare da bada tallafin kayan aiki ga asibitocin dake ƙananan hukumomin Garko da Wudil domin tallafawa harkar lafiya.

Taron ya samu halartar manyan baƙi da suka haɗar da wakilin gwamnan jihar Kano, Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso kuma mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin siyasa da wakilin Sanatan Kano ta Kudu Hon. Abdulrahman Kawu Sumaila da tsohon kakin majalisar jihar Kano mai girma Alhaji Gambo Sallau da kuma Alkasim Hussaini shugaban cibiyar koyar da sana’o’i ta Aliko Dangote.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sanarwa ta Musamman daga majalisar malaman Kano game da rasuwar Dantata

SANARWA MUHIMMIYA (GABATAR DA SALLATUL GA'IB) Assalamu Alaikum Warahmatullah, Sakamakon rasuwa...

Aminu Dantata ya bar mana wasiyyar inda za a binne shi – Iyalansa

Iyalan marigayi Alhaji Aminu Alassan Dantata sun shaida cewa...

Da dumi-dumi: Ganduje ya yi murabus daga shugaban jam’iyyar APC na kasa

Daga Abdullahi Shu Shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Umar...

Murtala Sule Garo Ya Taya Al’ummar Musulmi Barka da Shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1447AH

    Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano, Alhaji Murtala...