Majalisar ministocin Tinubu: Da amincewar shugaban PDP na kasa na zama Minista – Wike

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi ikirarin cewa jam’iyyar PDP ce ta ba shi damar karbar mukamin minista a karkashin gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

 

Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas, na cikin ministoci 45 da aka rantsar a hukumance a majalisar ministocin Tinubu a ranar Litinin.

Talla

Sai dai nadin na tsohon gwamnan ya janyo suka daga jama’a saboda kasancewar sa a jam’iyyar adawa ta PDP da kuma wata sanarwa da ya yi a baya da ke nuna rashin son zama minista bayan kammala wa’adinsa na gwamna.

 

A taron manema labarai na farko da ya yi a matsayin Ministan Babban Birnin Tarayya, Wike, ya ce Tinubu ya rubuta wa gwamnonin jihohi 36, ciki har da na PDP, wadanda a cewarsa, sun ba shugaban kasa sunaye 10 domin ya nada a matsayin ministoci.

Hakikanin Abun da ya faru a Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan Kano a zamanta na ƙarshe

Ya ce: “Ko za ka iya ambata wane ne maƙiyina? Ko za ka iya ambaton mutum guda maƙiyina?” Wike ya ce a taron manema labarai na farko.

“Duba, mutane suna ɗaukar farfaganda. Bari in yi amfani da wannan damar in gaya muku cewa ba na son mutanen da ba sa faɗin gaskiya. Sun ce za su sanya min takunkumi saboda na amince karbi karbi mukamin da aka yi min.

Kawu Sumaila ya ɗauki nauyin Karatun dalibai 100 a Kano ta Kudu

“Shugaban kasa ya rubuta wa gwamnonin jihohi 36 wasikar su kawo sunayen mutane goma da zai basu Muƙami, shin gwamnonin PDP ba su mika sunayen ba? Duk gwamnan PDP ya tura sunayen mutane goma domin a nada su mukami a gwamnatin tarayya .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gawuna ya mika ta’aziyyar rasuwar Alhaji Aminu Dantata

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna...

Nijeriya ta yi babban rashi: Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Aminu Dantata

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya...

Rasuwar Alhaji Aminu Dantata ta bar gibin da zai yi wuyar cikewa a Nigeria – Alhaji. Kabiru Sani Kwangila

Shugaban kamfanin gine-gine na SKY Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Sanarwa ta Musamman daga majalisar malaman Kano game da rasuwar Dantata

SANARWA MUHIMMIYA (GABATAR DA SALLATUL GA'IB) Assalamu Alaikum Warahmatullah, Sakamakon rasuwa...