Gawuna ya mika ta’aziyyar rasuwar Alhaji Aminu Dantata

Date:

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana alhinin sa bisa rasuwar dattijo, fitaccen ɗan kasuwa kuma mai bayar da gudunmawar al’umma, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, wanda ya rasu yana da shekaru 94 a safiyar Asabar, 28 ga Yuni, 2025.

A wata sanarwa da Gawuna ya sanyawa hannu da hannunsa wacce kuma aka aikowa Kadaura24, ya bayyana marigayi Dantata a matsayin wanda ya ba da gudunmawa sosai wajen ci gaban tattalin arzikin ƙasar.

InShot 20250309 102512486
Talla

“Alhaji Dantata zai ci gaba da kasancewa cikin tarihin Najeriya saboda kwazonsa, jajircewarsa, da kishin ƙasa da ya nuna ta hanyar gudanar da kasuwanci da ayyukan jin ƙai da suka taba rayuwar dimbin ‘yan Najeriya,” in ji Gawuna

IMG 20250415 WA0003
Talla

Gawuna wanda shi ne ya yi wa jam’iyyar APC takarar gwamna a zaben da ya gabata ya cewa “Marigayin ya shahara a harkar kasuwanci, kuma ya taka rawar gani a fagen hidimtawa jama’a, inda ya taba zama Kwamishinan Tsare-tsare da Ci Gaban Tattalin Arziki a tsohuwar Jihar Kano da sauran muhimman mukaman gwamnati.

Sanarwa ta Musamman daga majalisar malaman Kano game da rasuwar Dantata

Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan Dantata, Gwamnatin Kano da al’ummar jihar bisa wannan babban rashi, yana mai cewa Najeriya ta rasa ɗaya daga cikin fitattun ‘ya’yanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...