Musa Iliyasu Kwankwaso ya maka gwamnatin kano da wata hukuma a gaban kotu

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Tsohon kwamishinan ma’aikatar raya karkara Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso ya maka gwamnatin jihar kano da hukumar karɓar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa a gaban kotu bisa karɓar wata mota da ya saya daga hannun sa.

 

Musa Iliyasu Kwankwaso ya garzaya babbar Kotun jihar kano mai lamba 4 wadda ke karkashin mai Shari’a Usman Na’abba Inda ya bukaci wadanda yayi kara da su biya shi kudin da ya kashewa motar wajen gyara da kuma kudin da ya sayi motar ko kuma a mayar masa da motar.

Talla

Barr. Badaru Sulaiman Ishaq shi ne lauyan Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso da yake zantawa da manema labarai yace tun da fari ofishin Sakataren gwamnatin jihar kano ne ya rubuta wanda yake karewa cewar ya mayar da wata mota kirar Hilux wacca aka yi masa gwanjon ta tun a gwamnatin data gabata.

 

” Ya Sayi wata mota ne ta gwamnati wacce ta lalace a hannun wani kamfani da gwamnatin ta yiwa gwanjon motar, sai kawai yaga takardar ana bukatar ya mayar da motar, shi ne ya sanar da mu cewa mu rubutawa gwamnatin yadda akai ya mallaki motar”. A cewar Barr. Badaru

Hakikanin Abun da ya faru a Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan Kano a zamanta na ƙarshe

” Mun rubutawa gwamnatin takarda cewar bashi da ja zai mayar da motar, Amma ga kudin da ya kashewa mota, don haka zai mayar da motar wajen bakanikensa don a cire masa abubuwan da aka sanyawa motar, ya mayar wa bakaniken motar a kofar ruwa kawai sai hukumar karɓar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar kano ta turo aka dauke motar”. Inji Lauyan Musa Iliyasu Kwankwaso

Da dumi-dumi: NNPP Ta Maka Kwankwaso Kotu Bisa Zargin yiwa jam’iyyar Zagon Kasa

Yace Rashin basu amsa akan takarar da suka rubutawa gwamnatin ne yasa suka garzaya gaban kotu domin nemawa wanda suke karewa (Musa Iliyasu) hakkinsa.

Barr. Badaru Sulaiman ya kuma ce a yayin zaman Kotun, lauyoyin wadanda ake kara basu kaiwa kotun bayanan kariya ba, amma suna da ragowar kwanaki kamar yadda dokar ta bayyana.

Tuni dai Mai Shari’a Na’abba ya dage zaman sauraron karar zuwa ranar 16 ga watan October na shekara ta 2023 domin cigaba da Shari’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...